Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ceto wasu mutum biyu da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar.
Kakakin rundunar Mohammed Shehu wanda ya sanar da haka ya ce an ceto wadannan mutane bayan sun yi sati biyu a hannun ‘yan bindiga.
Shehu ya ce rundunar ta nasarar ceto wadannan mutane ne bayan bincike da bin sawun yan bindigan da dakarun suka yi har suka kai ga damke su.
Ya ce ‘yan bindigan sun yi garkuwa da wadannan mutane daga kauyen Magami dake karamar hukumar Kaura Namoda da kuma wasu daga dazukan Dumburum da Gidan Jaja a karamar hukumar Zurmi.
Shehu ya ce bayan likitoci sun duba su rundunar za ta gana da mutane inda daga nan a koma da su garuruwan su.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ayuba N. Elkanah ya tausaya wa mutanen sannan ya yi kira ga sauran mutane da su hada hannu da jami’an tsaro domin ganin an kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga a jihar.
Zamfara, Kaduna, Katsina, Kebbi da Sokoto a Arewa maso Gabas da jihar Niger dakedake Arewa ta Tsakiya na cikin jihohin dake yawan fama da aiyukkan ‘yan bindiga a Najeriya.
Duk da tsauraran matakan da gwamnatocin jihohin suka dauka domin ganin sun dakile aiyukkan mahara ‘yan bindiga su ci gaba da kisa da yin garkuwa da mutane a jihohin.