Wata matan aure mai suna Naja’atu Lawal ta kai karar mijinta Isa Yusuf a kotun shari’a dake Magajin Garin Kaduna domin kotu ta raba auren su saboda rashin mutuncin da Yusuf ya yi mata.
Naja’atu wacce ke zama a unguwan Rimi ta bayyana wa kotu cewa mijinta Yusuf baya kula da ita da ‘ya’yan su biyar shekaru biyu kenan ya kama gabansa
“A wannan lokaci ni ce sutura, abinci, wurin kwana da kudin makaranta.
Naja’atu ta ce bayan shekara biyu sai Yusuf ya dawo sannan ya kirata ta zo ta karbi takardar saki.
Ta ce ko da ta isa wurin sa ta karbi sakin da ya ce ta zo ta karba, sai Yusuf ya afka mata ya hauta da duka, sai da yayi mata tilis ya yayyaga mata gyale sannan kuma bai bata takardar sakin ba.
Naja’atu ta roki kotun da ta raba wannan aure ba za ta iya ci gaba da zama da shi ba.
Yusuf wanda ke aikin wanki da guga a Badarawa ya bayyana wa kotu cewa dalilin da ya sa bai iya kula da matar sa da ya’yan su biyar ba shine don fama da yayi da rashin lafiya na tsawon shekara daya da rabi a can gidan iyayen sa ya yi jinya.
Ya ce da ya samu lafiya sai ya dawo gida wajen iyalinsa amma sai bai gan su ba a gidan hayan da ya kama musu.
Yusuf ya ce yanzu komai zai dai-daita saboda ya yi lafiya sannan yana zuwa aiki yana samun kudi.
Alkalin kotun Nuhu Falalu bayan ya saurari ma’auratan ya daga shari’an zuwa ranar 15 ga Nuwanba.
Falalu ya ce Naja’atu za ta gabatar da shaidu a kotun domin tabbatar da duka abinda ta fadi a gaban kotu.
Discussion about this post