Daya ga watan October, ita ce ranar da kasar Najeriya ta cika shekara 61 da samun ‘yancin kai. Allah mun gode maka, gamu a cikin wannan rana da ranmu da lafiya. Wasu daga cikinmu, a gabansu aka samu ‘yancin kai, yanzu ba sa raye. Mu ‘ya’ya da jikokinsu muna duniya har yanzu. Wannan arziki ne babba. Alhamdulillah!
Allah ya jikan magabatanmu. Tun suna da rai ake cikin gwagwarmayar gyaran Najeriya. Abun mamaki, turawa suna bamu ‘yanci sai mu ka fara cutar junanmu. Gwamnati ta farko da aka kafa, a qarqashin tsari irin na Ingila, wanda ake kira da turanci “Parliamentary system”, bai je ko ina ba saboda bayahudiyar hassadar juna. Tun daga d’aya ga watan October a 1960, Najeriya ta fara shiga rud’ani, gashi nan har yanzu ana ta fama. An kafa gwamnatin su Tafawa Balewa amma wasu suna shirin kifar da ita a 6oye. Ka karanta littafina saboda samun fa’ida (The Best Way To Survive In Nigeria).
Rannan ina karatu sai na ci karo da wasu abubuwa na siyasar jamhuriya ta biyu. A lokacin mulkin Marigayi Alhaji Shehu Shagari. Allah ya jikansa. Abubuwan da jam’iyarsa (NPN) ta yi kamfen da su a 1979, tabbas ba su da bambanci da wad’anda jam’iyyun PDP da APC su ke yin kamfen da su ba a cikin wannan jamhuriyar ta hud’u. Ba a maganar jamhuriya ta uku ma ta shekarar 1993, wacce masana kimiyar siyasa su ke yi mata kallon ungulu da kan zabo.
Akwai bukatar cewa, duk sanda zamu yi farin cikin zagayowar ranar ‘yancin kai, to mu kasance cikin murnar samun cigaba sosai, ba cigaban mai hakan rijiya ba. Muna kara tsufa, wahalarmu tana karuwa. Kwanakin baya zan shige, sai na ga matasa da riguna suna ta shirin bikin ranar ‘yanci. Sai na siyi gud’a 5 nace a rabar da su don a bayyana farin ciki amma zuciyata cike take da takaici saboda halin da siyasarmu take ciki yanzu.
Duk da haka, ina taya kasar Najeriya murnar zagayowar ranar ‘yancin kai. Muna fatan, watarana za mu samu gyara a cikinta. Duk da akwai mutane da yawa da su ka cire rai da samun gyara. Wannan shi ne yake haifar da qauracewa siyasa (political apathy). Hakan kuma ba daidai bane. Idan ku ka daina za6e, masu rauni ne daga cikinku zasu dinga za6o muku irinsu.
Allah ya shiryar da mu.