Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya umarci hukumar sadarwa ta kasa ta buɗe layukan sadarwa a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Kakakin gwamnan jihar Bappa Zailani ya fitar da wannan sanarwa ranar Juma’a ya na mai cewa gwamnati ta yi haka ne domin mutane su sami saukin wahalhalun da suka afka ciki a dalilin rashin aikin hanyoyin sadarwar a jihar.
” Sake buɗe hanyoyin sadarwa a jihar ya zama dole yanzu ganin irin nasarorin da aka samu a ragargazar ƴan bindiga da jami’an tsaro suka yi a faɗin jihar.
Zailani ya kara da cewa a dalilin waɗannan nasarori da aka samu yasa gwamnati ta umarci hukumar sadarwa ta ƙasa ta bude layukan kira a garin Gusau.
Nasarorin da muka samu a jihar Zamfara
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Zamfara Ibrahim Dosara ya bayyana cewa an samu nasarori masu yawa a yakin da ake yi da ƴan bindiga a faɗin jihar tun bayan sassaka dokoki da akyi domin kawo karshen su.
Da yawa daga cikin ƴan bindigan sun arce sun fice daga jihar saboda tsaninin azabar jami’an tsaro da kuma yunwa da ta nemi ta kashe su, “Ya fa kai ga ko abinci basu iya dafawa sai da su ci shi danye.
” Yanzu saboda azabar da suke sha da kuma farautarsu da sojoji ke yi, a rakuma suke baddakama suna kai hare-hare a wasu kauyuka.
”
Discussion about this post