Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya soki tsarin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje da Babban Bankin Najeriya ta bijiro da shi, wanda ya haddasa hauhawar farashin Dalar Amurka da Fan na Ingila.
Osinbajo ya ce ya kamata CBN ya canja tunani, tare da kira ga shugabannin bankin su sake fito da tsarin da zai kare darajar Naira.
Da ya ke jawabi wurin taron bita da bibiyar ayyukan ma’aikatun gwamnati a ranar Litinin a Abuja, Osinbajo ya ce farashin canji ya yi ƙasa ƙwarai, bai yi daidai da halin da kasuwa ta ke ciki ba a yanzu.
A yanzu dai Naira 414 ake sayar da dala ɗaya a farashin gwamnati. A kasuwar ‘yan canji kuma ana sayar da ita Naira 570.
“Saboda idan farashin canji ya yi ƙasa, to ba mu iya samun sabbin daloli kuma. Saboda haka akwai buƙatar shugabannin CBN su sake tunani. Amma dai na san idan Gwamnan CBN ya samu lokaci, zai yi bayani a kai.”
Osinbajo ya danganta matsalolin tattalin arzikin da ake fuskanta da ƙarancin kuɗaɗen canji na ƙasashen waje, saboda hakan ya haddasa ba a iya shigo da kayan ayyukan da sai a ƙasashen waje ake iya samun su.
Daga nan ya yi nuni da cewa CBN ya na aiki ne kamar ya na takara ko nuna kishi da wasu ma’aikatun gwamnati ko hukumomi.
Daga nan sai ya yi kira da a riƙa samun fahimtar juna da yin ayyuka tare, tsakanin CBN da ma’aikatun gwamnati.
Ya yi tsokaci a kan wasu ayyuka ko shirye-shiryen da CBN ke gudanarwa, waɗanda a zahiri wasu ma’aikatu ne ya kamata su riƙa aiwatar da su, ba CBN ba.
“Kamata ya yi a ce Ma’aikatar Kasuwanci da Zuba Jari ce za ta tafiyar da raba tallafin Ƙanana Da Matsakaitan Masana’antu (MSME), ba CBN. Idan ma CBN ne ke yin aikin, to kamata ya yi a riƙa yi tare da wannan ma’aikata.
“Saboda wasu lokuta sai ka ga an bai wa wasu mutane tallafin fiye da sau ɗaya. Domin babu cikakken tsarin da ake bi domin daddale waɗanda aka baiwa ko sanin abin da ake ciki.”