Aƙalla kwangiloli har 878 ne Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bayar, tun daga hawan ta mulki ranar 39 Ga Mayu, 2015 zuwa yanzu.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ne ya bayyana haka, a wurin Taron Tsakiyar Shekara da Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya ke yi, domin duba irin nasarorin da kowace Ma’aikata da Hukumomi su ka samar a cikin watanni shida na farkon shekara.
Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin sa Yemi Osinbajo da dukkan Ministoci da Shugabannin Hukumomin Gwamnantin Tarayya duk sun halarci taron.
Boss Mustapha ya ƙara da cewa Gwmnatin Buhari ta bijiro da tsare-tsare guda 319, yayin da ta karɓi bayanan ayyukan gudanarwa 206, inda jimilla su ka tashi ayyuka 1403 kenan.
Haka kuma Boss Mustapha ya ce tsakanin ranar 29 Ga Mayu, 2019 zuwa Agusta 31, Gwamnantin Buhari ta yi zaman Majalisar Zartaswa na Ministoci sau 52.
Sakataren Gwamnatin Tarayya dai bai fayyace yawan aikin kwangilolin da aka yi a kowace ma’aikata ba. Amma ya ce dukkan ayyukan na raya ƙasa ne.
Sai dai kuma duk wa yawan ayyukan da Boss Mustapha ya ce gwamnatin Buhari ta bayar a matsayin kwangila, wasu yankuna da shiyyoyi da ma ɗaiɗaikun jihohi ana ƙorafin cewa Gwamnatin Buhari ba ta yi masu halacci ba.
Matsalar tsaron da ta kassara jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna, Sokoto, Neja da wasu yankuna na Jihar Kebbi ya sa wurare da yawa ba a ganin wani abin a zo a gani da za a jinjina wa Gwamnatin Buhari, a tsawon sama da shekaru shida bayan hawan sa mulki.
Discussion about this post