TSUNTSUN DA YA KIRA RUWA: APC ta fatattaki jigon ta wanda ya yi wa Buhari fatan yin mutuwar cutar korona

0

Uwar jam’iyyar APC ta kori Shugaban Riƙo na APC na Ƙaramar Hukumar Yola ta Kudu, a Jihar Adamawa, mai suna Sulaiman Adamu.

Tun a farkon watan Agusta ne dai aka fara dakatar da shi, bayan fallasa wata muryar sa da ya ke wa Shugaba Muhammadu Buhari fatan Allah ya sa cutar korona ta kashe shi.

Tun lokacin dakatarwar dai Kakakin Yaɗa Labarai na APC a Jihar Adamawa, Mohammed Abdullahi ya bayyana cewa kalaman na Sulaiman abin damuwa ne matuƙa. Ya ce za su yi bincike.

“A kan haka, an kafa kwamitin mutum bakwai domin su binciki muryar kuma su gabatar da irin hukuncin da ya dace a ɗauka.

“An amince ya sauka daga shugabancin APC na Ƙaramar Hukumar Yola ta Kudu, har sai bayan kammala bincike tukunna.”

A taron da uwar jam’iyya ta yi a ranar Alhamis, ta yi amfani da ƙarfin yaƙinin kwamitin bincike, wanda su ka tanadi irin ladabtarwar da su ka tanadar a yi masa.

“Daga yau ɗin nan an kore shi daga jam’iyya kwata-kwata.”

Haka uwar jam’iyyar ta sanar a cikin wani kwafen jawabi da Sakataren Riƙo na ƙasa John Akpanudoedehe ya sa wa hannu.

Sakataren ya ce rashin mutuncin da Adamu ya yi wa Shugaba Buhari zai iya zubar da ƙimar APC a ƙasa nan kuma a riƙa yi wa shugabannin ita wannan jam’iyya kallon waɗanda ba su san ta kan shugabanci ba.

Ba Kan Sa Farau Ba:

Idan ba a manta ba, Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya kori wani hadimi kuma ɗan lelen sa, Salihu Tanko, saboda ya ci mutuncin Shugaba Muhammadu Buhari a soshiyal midiya.

Share.

game da Author