Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo a Kudu maso Kudu, ya bijire wa umarnin kotu, inda ya tubure cewa sai wanda aka yi wa rigakafin cutar korona kaɗai za a bari ya shiga masallaci, coci-coci, bankuna da sauran wuraren haɗuwar jama’a.
Wannan matsaya ta sa dai ta ci karo da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Fatakwal ta yanke, cewa Obaseki ya jingine wannan umarni na sa har sai kotun ta gama bin ba’asin ƙarar da aka shigar cewa umarnin ya take haƙƙi ɗan adam.
Sai dai shi kuma Obaseki a ranar Laraba da ta gabata, ya shaida wa manema labarai cewa matsawar jama’a su ka ƙi bin umarnin bin ƙa’idoji da sharuɗɗan kiyaye kamuwa ko watsa cutar korona a cikin jama’a, to zai ƙaƙaba dokar kullen korona kawai.
Obaseki ya shawarci duk wasu masu taro na addini ko na bukukuwa ko na kasuwanci, su tabbatar waɗanda za su halarta sun yi rigakafin korona, kuma su na ɗauke da katin shaida.
Sai dai kuma masu ƙorafi da wannan umarni na ganin cewa kakkausan kalaman gwamnan na nuni da tilasta wa jama’a yin riga-kafi da sun ƙi da sun so a bisa dolen-dole kenan.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Babbar Kotu ta hana Gwamna ƙaƙaba dokar shiga masallatai da coci-coci da katin shaidar rigakafin korona.
Babbar Kotun Fatakwal da ke Jihar Ribas ta dakatar da Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo daga ƙaƙaba dokar hana shiga masallatai da coci-coci sai da katin shaidar rigakafin korona.
Cikin wani hukunci da Mai Shari’a Stephen Pam ya yanke a ranar 30 Ga Agusta, ya ce kada Gwamna Obaseki ya ƙaƙaba dokar, har sai an gama sauraren ƙarar da Babban Lauya Echezona Etiaba ya shigar a madadin mai ƙara Charles Oseretin.
Oseriten ya nemi a hana Obaseki ƙaƙaba dokar tilasta wa mutane a danƙara masu rigakafin korona da kuma hana su shiga wuraren ibadu da sauran wuraren hada-hada idan ba su da katin shaidar rigakafin korona.
Ya ce wannan take masu ‘yancin ɗan adam ne Gwamna Obaseki ke neman yi.
Mai Shari’a ya sa ranar 10 Ga Satumba zai yanke hukunci.
Ranar Lahadi ce wannan jarida ta ruwaito Gwamna Obaseki ya hana shiga masallatai, coci-coci da bankuna sai da katin shaidar rigakafin korona.
Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo ya hana Musulmai da Kiristoci shiga masallatai da coci-coci ba tare da katin shaidar an yi wa mutum rigakafin korona ba.
Wannan doka ta shafi shiga bankuna da sauran wuraren da dandazon jama’a ke taruwa.
Obaseki ya yi wannan bayani a Benin, babban birnin jihar, a lokacin da ya ke ƙaddamar da fara yin allurar korona kashi na 2 a jihar.
“Daga makonni biyu na farkon watan Satumba za a hana shiga masallatai da coci-coci da bankuna da sauran wuraren ayyukan gwamnati ga duk wanda ba a yi wa rigakafin korona ba.
“Alamomi sun nuna tabbas korona ta samu gindin zama cikin jama’a daram-daƙam. Kuma babu wanda zai iya cewa wani nau’in korona bayan wannan na ‘Delta Varient’ ba zai iya bayyana ya fantsama ba.
“Saboda haka mu ba za mu sake kulle Jihar Edo ba, amma dai za mu hana duk wanda ba a yi wa rigakafi ba shiga cikin jama’a a wuraren ibada, ma’aikatu da sauran wuraren da jama’a ke hada-hada, kamar bankuna da sauran su.”
Obaseki ya ce tuni an tsara komai yadda jami’an tsaro za su riƙa hana wanda bai ɗauke da katin shaidar korona shiga masallatai da coci-coci da sauran wuraren taruwar jama’a.”
Gwamnan ya nuna damuwa ganin yadda cutar korona ke ƙara bazuwa a jihar
Edo.
Ya ce gwamnatin sa za ta yi ƙoƙarin ganin an yi wa aƙalla kashi 60% cikin 100% na ‘yan jihar Edo rigakafin korona nan da ƙarshen shekara mai zuwa.