SABON TSARI: Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya za su fara more abinci mai gina jiki

0

Gwamnatin Tarayya ta amince da ɓullo da shirin Samar da Abinci mai Gina Jiki ga Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.

Shirin mai suna National Policy on Food and Nutrition, Kakakin Shugaban Ƙasa Garba Shehu ne ya sanar da amincewa da shi bayan kammala Taron Majalisar Zartaswa a ranar Laraba, a Fadar Shugaban Ƙasa.

Shehu ya ce ɓullo da shirin na nufin za a riƙa ware kuɗaɗe a cikin kasafin kuɗin kowace Ma’aikata, Hukumoni da Cibiyoyin Gwamnantin Tarayya waɗanda da su za a riƙa samar da abinci mai gina jiki ga ma’aikatan ɓangaren.

“A yau Majalisar Zartaswa ta amince a ɓullo da shirin samar wa ma’aikatan gwamnatin tarayya abinci mai gina jiki. Kuma ana sa ran shiri nan gaba zai haɗa da gwamnatin jihohi da na ƙananan hukumoni.”

Ya ce tsarin zai tabbatar da an samu ingancin lafiya da abinci mai gina jiki ga ma’aikata, kamar yadda Yarjejeniyar Inganta i Ma’aikatan Ƙwadago ta ILO ta tabbata cikin 2006.

Garba Shehu ya ƙara da cewa tsarin wani hoɓɓasa ne wajen inganta kiwon lafiyar ma’aikata, kare lafiyar su da inganta rayuwar su ta hanyar samar masu abinci mai gina jiki.

“Hakan ya na nufin gwamnatin Najeriya ta fara ɗaukar matakin bin ƙa’idar yarjejeniyar Kungiyar Ƙwadago ta Dunya (ILO), wadda ƙasashen duniya su ka cimma tun a cikin 2006.

“Dama tun a lokacin Najeriya na cikin ƙasashen da su ka kaɗa ƙuri’ar amincewa da shirin. Yanzu kenan za a fara amfani da yarjejeniyarin s Najeriya.” Inji Shehu.

Garba Shehu ya kuma ce Majalisar Zartarwa ta amince da ware kuɗi naira biliyan 1.2 domin yin gyaran gaggawa a harkokin bayar da ruwan sha a jihar Nassarawa.

Ya ce wannan buƙatar gaggawa ta taso ne sanadiyyar ɓarnar da ambaliya ta yi wa bututun aika ruwa masu yawan gaske a jihar.

“Tun a cikin 2000 ne wata ambaliya ta lalata garin Nasarawa tare da lalata hanyar samar da ruwan garin baki ɗaya.”

Ya ce Gwamnatin Tarayya ta shiga lamarin, saboda Gwamnantin Jihar Nasarawa ta kasa gyara wannan gagarimar matsalar samar da ruwa a garin.

Share.

game da Author