Shugaban hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC Chikwe Ihekweazu ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar korona yayin da suke ci gaba da harkokin rayuwar su domin cutar ta zo ta zauna.
Ihekweazu ya fadi haka ne yayin da yake karfafa gwiwowin mutane kan yin gwajin cutar korona da yin allurar rigakafin korona a taron da kwamitin PSC ta yi da manema labarai ranar Litini a Abuja.
“Muna kira ga mutane da su ci gaba da mara wa gwamnati baya a yakin da take yi da korona ta hanyar kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar.
Ya ce zuwa yanzu mutum miliyan 229 ne suka kamu da cutar inda daga ciki mutum sama da miliyan 4.7 sun mutu.
“Makarantu a wasu kasashen sun fara karatu, ana tilasta mutane saka takunkumin fuska da yin allurar rigakafin korona yayin da zazzafar nau’in korona ‘Delta’ ta ci gaba da yaduwa kamar wutan dare a duniya.
“Domin samun nasaran dakile yaduwar cutar wasu kasashen duniya har yara masu shekara 12 zuwa sama suke wa allurar rigakafin korona.
Ihekweazu ya ce a Najeriya mutum sama da 200,000 ne suka kamu da cutar inda daga ciki mutum 2,600 sun mutu.
Ya ce hukumar NCDC za ta ci gaba da hada hannu da hukumomin kiwon lafiya ta duniya domin karo yawan maganin rigakafin cutar da hanyoyin dakile yaduwar cutar a kasar nan.
A taron da PCS ta yi ranar Litini shine ranar karshe da Ihekweazu zai rike shugabancin hukumar NCDC.
Ihekweazu zai ci gaba da aiki da Hukumar lafiya ta duniya WHO a matsayin mataimakin shugaban fannin dakile yaduwar cututtuka ranar daya ga Nuwamba.