Gwamnatin tarayya ta soke fasfo din matafiya 2,000 na tsawon shekara daya a dalilin sabawa ka’idojin tafiye-tafiye da suka yi wadanda suka shafi Korona.
Gwamnati ta kama wadannan matafiya da laifin kin killace kansu na tsawon kwanaki 14 bayan sun shigo kasar nan daga kasashen waje.
Mukhtar Muhammad, ya bayyana haka a taron kwamitin PSC da manema labarai a Abuja ranar litinin.
Muhammed ya ce har yanzu gwamnati na nan a kan bakanta na ganin cewa duk matafiyan da suka shigo kasar nan musamman daga kasashen da cutar ta tsanani sai sun killace kansu a wuraren da gwamnati ta bada na tsawon kwanaki 14.
Ya ce banda soke fasfo din matafiyan gwamnati ta yi, za ta buga sunayensu a wuraren killace mutane da gwamnati ta bude.
Sannan kuma gwamnati za ta hukunta masu siyar da maganin rigakafin da katin shaidan allurar korona wanda ba a basu lasisin yin haka ba.
Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya ce gwamnati ta dauki ma’aikatan da za su rika duba takardu, magungunan rigakafi da katin shaidan yin allurar rigakafi a duk asibitocin dake yi wa mutane allurar rigakafin korona a kasar nan.
Bayan haka Shu’aib ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina yada jita-jita game da ingancin maganin allurar rigakafin korona da ake yi wa mutane a kasar nan.