Jami’in fannin abincin dake inganta garkuwar jiki na ma’aikatar lafiya dake jihar Ebonyi Cyprian Ogbonna ya ce akalla yara 20,000 ne ke mutuwa duk shekara a jihar a dalilin fama da tsananin yunwa.
Ogbonna ya fadi haka ne a taron tattauna hanyoyin kawar da yunwa a yara da aka yi a Abakaliki.
Ya ce gwamnati za ta iya ceto yara daga matsalar yunwa idan ta wayar da kan mutane musamman na yankin karkara mahimmancin ciyar da ‘ya’yan su abincin dake gina garkuwar jiki.
Bayan haka wasu kwararrun jami’an lafiya da suka halarci taron sun yi kira ga gwamnati da ta mai da hankali wajen dakile yaduwar cututtuka yayin da take yaki da kawar da yunwa a jikin yara kanana.
Sun ce cututtuka da suka hada da korona, zazzabin cizon sauro, kanjamau, Kwalara na ciki cututtukan dake kisan yara a jihar.
Babban jami’in dake kula da fannin dakile zazzabin cizon sauro a ma’aikatar Lafiya ta jihar Lawrence Nwankwor ya ce gwamnati za ta kara yawan kudaden da take warewa don yaki da zazzabin cizon sauro domin samun raguwar yaduwar cutar.
“Za a yi nasarar kawar da cutar ne idan mutane sun tsaftace muhallin su tare da yin amfani da gidajen sauro.
Shima shugaban fannin yin allurar rigakafi a ma’aikatar John Nkwuda ya ce gwamnati na kokarin ganin ta kawar da cututtukan dake kisan yara kanana ta hanyar inganta yin allurar rigakafi a jihar.