Wasu matasa ɗauke da muggan makamai sun tare wasu manyan motocin bas mai cin mutum 18 a hanyar Jos zuwa Zaria inda suka far musu suka kashe akalla mutum sama da 20, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
Daily Nigerian wanda ta ce wakilinta ya ziyarci wannan wuri bayan wannan mummunar abu ya auku.
Ya ce matafiyan na dawowa daga taron murnar shiga sabuwar shekarar musulunci wanda aka yi a garin Bauchi bisa gayyatar Sheikh Dahiru Bauchi, kamar yadda Ibrahim wanda ya tsira daga wannan hari ya bayyana.
Majiyar ta bayyana cewa koda motocin suka isa gada-biyu dake karamar hukumar Jos ta Arewa sai matasan suka dira musu, suka fara sara suna duka.
” Mutum sama da 80 sun arce cikin daji. Sannan kuma na ga wasu gawarwaki har 22 waɗanda na ƙirga da kai na a asibitin koyarwa na jami’ar Jos.
Discussion about this post