Kotu a Jihar Kano ta yanke wa yar wasan Hausa Sadiya Haruna komawa makarantar Islamiyya bayan ta kamata da laifin yada hutonan batsa a shafinta na yanar gizo
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ce ta kama da kuma garkame jarimar ƴar wasan Kannywood da kuma ta yi fice a kafar sada zumunta, kan yaɗa hotunan batsa a shafukanta na sada zumunta.
Alkali Ali Danzaki ya yanke mata hukunci tare da umartar ta koma Islamiyya tayi karatu na tsawon wata shida.
Sannan ya ce a kullum za ta riƙa zuwa Islamiyyar da rakiyar jami’in Hisbah domin tabbatar da cewa hukuncin yayi tasiri.
Sadiya ta amsa laifi guda cikin tuhume-tuhumen da aka gabatar a kanta, wanda ya tsaba wa sashi na 355 na kudin panal code na 2000.
Alkalin na kotun kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Sharada, yace Sadiya zata koma makarantar Darul Hadiths dake a unguwar Tudun Yola a cikin Birnin Kano.
Discussion about this post