Yadda cikin mu ya duru ruwa bayan kutsawa NDA da ‘yan bindiga suka yi – Mazauna garin Kaduna

0

Mutanen garin Kaduna sun bayyana yadda suka shiga cikin rudani da fargaba bayan jin labarin kutsawa da yan bindiga suka yi cikin barikin NDA, suka kashe manyan sojoji biyu sanna suka arce da babban jami’i daya.

PREMIUM TIMES HAUSA ta tattauna da wasu dake makwabtaka da NDA a Kaduna inda suka nuna rashin jin dadin su game da abinda ya faru da kuma fargabar cewa lallai tsaro ya tabarbare a jihar da kasa baki daya.

Balele Sani, ya bayyana cewa shi a ganin shi an shiga cikin tsananin rashin tsaro a kasar nan da rudanin gaske.

” Kowace kasa da sojojin ta suke takama amma kuma ace ya kauga ‘yan bindiga za su iya kutsawa cikin wuri irin NDA su kashe manyan sojoji sannan su fice salin alin, abu ya baci kenan.

Sahura Alkali cewa ta yi abin ya saka ta cikin wani yanayi na rashin natsuwa tun bayan aukuwar abin.

” Ni dai gaba daya har yanzu a cikin yanayi na rashin natsuwa na ke. Ga mu ga NDA, da wurin muke takama amma yanzu suma ba su tsira ba. A ce har ‘yan bindiga su kutsa cikin barikin sojojin da kasa ke ta kama da su yi kisa sannan su arce da babban soja ga shi ana neman a kwana ba a iya kaiwa garesu ba, dole hankali na ya tashe matuka. Abu dai ya tabarbare kawai.

Haka mutane da dama da suka tattauna da PREMIUM TIMES Hausa suka rika rika fadi.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda yan bindiga sanye da kayan sojoji suka yi kukan kura suka kutsa barikin NDA suka kashe jami’ai biyu sannan suka sace wani babban soja daya.

Jihar Kaduna kamar wasu jihohin yankin Arewa Maso Yamma na fama da hare-haren yan bindiga da garkuwa da mutane.

Har yanzu makarantun jihar na kulle saboda rashin tsaro da yayi tsanani a jihar.

Share.

game da Author