Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa mutum 2,037 ne suka kamu da cutar korona sannan cutar ta yi ajalin mutum 25 daga ranar Litini zuwa Alhamis a Najeriya.
Najeriya ta ci gaba da samu yaduwar cutar tun bayan da hukumar ta sanar da bullowar zazzafar nau’in cutar ‘Delta’.
A ranar Litini mutum 565 ne suka kamu sannan mutum 8 sun mutu a kasar nan.
Mutum 637 sun kamu, mutum 7 sun mutu ranar Laraba.
A ranar Alhamis mutum 835 sun kamu sannan mutum 10 sun mutu.
Zuwa yanzu mutum 189,715 ne suka kamu mutum 2,298 sun mutu a kasar nan.
An sallami mutum 169,626 sannan mutum 17,791.
Idan ba a manta ba a ranar Litinin din da ya gabata ne gwamnati ta fara yi wa mutane allurar rigakafin korona zango na biyu da maganin rigakafin na ‘Moderna’ wanda kasar Amurka ta bai wa kasar nan kyauta.
Bayan haka gwamnati ta kuma karbi kwalaben maganin rigakafin na Johnson & Johnson guda 177,600 daga hannun AU.
Daga nan gwamnati ta karbi kwalaben maganin rigakafin na Oxford-astraZeneca guda 699,760.
Gwamnati ta ce za ta yi amfani da maganin Oxford-astraZeneca da ta karba domin karike yi wa mutanen da suka yi allurar rigakafin da ruwan maganin a zango na farko.
Zuwa yanzu an yi wa mutum 3,966,005 allurar rigakafin cutar korona a kasar nan inda daga ciki mutum sama da miliyan biyu sun yi. allurar rigakafin zango na biyu.
Gwamnati ta yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da korona domin samun kariya.
Sannan gwamnati ta yi kira ga wadanda basu yi allurar rigakafin korona ba da su hanzarta zuwa wuraren da ake yin rigakafin domin kare kansu da na kusa da su daga kamuwa da cutar.