FILAFO TA ƊAU ZAFI: Ka kawo karshen kashe-kashen da ake yi nan da makonni biyu – Majalisa ga Gwamna Lalong

0

‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Filato sun umarci Gwamna Simon Lalong na jihar cewa sun ba shi wa’adin makonni biyu ya kawo ƙarshen kashe-kashen da ake yi a faɗin jihar.

Sun kuma umarci mazauna cikin yankunan karkara da ake kai wa hare-hare su tashi su riƙa kare kan su, saboda gwamnati ta kasa kare rayukan su.

Philip Dasun wanda shi ne Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai ya sanar da wannan matsayar da ‘yan majalisar su ka ɗauka, a lokacin da ya ke wa manema labarai jawabi a Jos.

Dasun ya ce ‘yan majalisar za su yi tunanin mataki na gaba da za su ɗauka, bayan cikar wa’adin makonni biyu ɗin da su ka bayar na neman kawo ƙarshen kashe-kashen da ke addabar jihar.

“A matsayin mu na ‘Yan Majalisar da ke da kishin al’ummar su a cikin zukatan su, mu na kira ga ɗaukacin jama’ar Jihar Filato su ƙarara ba mu yaƙinin aikin da mu ke yi domin su.

“Mun bayar da wa’adin makonni biyu a kan magance taɓarɓarewar tsaro tare da kawo zaman lafiya mai ɗorewa.

“Mu na kira ga Gwamna Simon Lalong Baƙo ya fito da bayanin kare mu a matsayin al’umma domin sake wanzar mana da zaman lafiya.

“Mu na kuma kira da babbar murya ga al’ummar jihar Filato su tashi su kare kan su, saboda tsarin samar da tsaro daga jami’an tsaro ya kasa samar mana da tsaron rayukan mu.” Inji Honorabul Dasun.

Sanarwar ta kuma yi kira ga sarakunan gargajiya su fito da tsarin samar da zaman lafiya ta hanyar kare kai da kuma tilasta sa-idon masu bijilanti, maharba da mutanen cikin karkara masu hikima.

Majalisar ta umarci Shugabannin Ƙananan Hukumomi su dakatar da shirin ɗaukar malaman wucin-gadi, maimakon haka, a ɗauki ‘yan bijilanti 200 a kowace ƙaramar hukuma domin ƙarfafa ayyukan sa-kai da binciko bayanan sirrin da su ka danganci matsalar tsaro.

Majalisar ta kuma yi kira ga jami’an tsaro su zaƙulo waɗanda ke karkashe mutane su kama su, domin doka ta hukunta su.

“A madadin ‘Yan Ina miƙa ta’aziyya da jaje ga gwamnatin jihar Filato, al’ummar yankunan Bassa, Barkin Ladi, Bakkos, Jos ta Arewa, Jos ta Kudu, Mangu, Riyom, Jami’ar Jos da kuma na Yelwa Zangam.”

Share.

game da Author