RUWA BA YA TSAMI BANZA: Ledar ‘pure water’ ta koma naira 20 a Jihar Nasarawa

0

Ƙungiyar Masu Sarrafa ‘Pure Water’ ta Jihar Nasarawa (ATWAP) ta bayyana cewa kwanan nan za ta maida duk leda ɗaya ta ruwan ‘pure water’ naira 20 a jihar.

Shugaban Ƙungiyar Usman Diggi na yankin Keffi da Mararaba ne ya bayyana haka, inda ya danganta tsadar ruwan da tsadar kayan haɗin ruwan kafin a sarrafa shi.

Ya yi bayanin a Ƙaramar Hukumar Karu, lokacin wani taron bita na sanin makamar aiki na kwana biyu da aka shirya.

Ya ce saboda tsadar kayan aiki, za a daina sayar da ‘pure water’ naira 10, zai koma naira 20.

Ya ce tsadar kayan aikin haɗin sarrafa ‘pure water’ ce ta sa ake samun yawaitar ruwan sha maras inganci na ‘pure water’ a yankin.

Diggi ya bayyana cewa abin takaici ne halayyar wasu mambobin da har su ke rage wa ruwan da su ke sayarwa inganci.

“Babu daɗi ko kaɗan a ƙara farashin ‘pure water’ daga naira 10 zuwa naira 20. Amma kuma har gara a ƙara farashin a riƙa yin sa da inganci. Ƙari ya zama dole, domin idan ba a sayar naira 20, to asara za a riƙa yi.”

Ya ƙara da cewa samar da ‘pure water’ maras inganci babbar barazana ce ga lafiyar jama’a.

Diggi ya roƙi gwamnati ta yi iyar ƙoƙarin ganin ta rage farashin kayan haɗin ‘pure water’ domin farashin sa ya tsaya daidai yadda ya ke, wato naira 10 kacal.

“A baya naira 450 ake sayar da duk kilo ɗaya na ledar da ake ɗura ‘pure water’. Amma a yanzu haka ta kai naira 1,200. Amma kuma babbar ledar ruwan naira 60 ko 70 ake sayar da ita har yanzu.

“Mu da mu ke sarrafa ‘pure water’ asara kaɗai mu ke yi. Yawancin masu harkar sai sun yi tsambare ko algusshu, domin su samu su ci riba.” Inji Diggi.

Sai dai kuma ya ce ƙungiyar su ta na bakin ƙoƙarin ganin ta magance matsalolin masu rage wa ruwa daraja da ingancin sa.

Ya ce ɗimbin masu sayar da ‘pure water’ sun watsar da sana’ar, saboda asara kaɗai su ke ɗibgawa.

Share.

game da Author