Shirin ciyar da yaran makarantan firamare daga aji 1 zuwa 3 da gwamnatin tarayya ke yi a jihar Kano ya cilla daga yara miliyan 1.2 zuwa miliyan 2.1.
Kwamishinan ilimin jihar Muhammad Salisu-Kiru ya sanar da haka a jawabin da ya yi a taron shirin ciyar da ɗaliban makarantar Firamare da aka yi a ma’aikatan ilmi na jihar ranar Asabar.
“Na kafa kwamiti domin tanttance alkaluman yawan yaran makarantan domin samun amincewar gwamnatin tarayya.
Kiru ya ce masu ruwa da tsaki a fannin ilimi dake kananan hukumomin jihar, sakataren ma’aikatar ilimi, shugaban hukumar SUBEB duk suna suna bin digginn samunin uawan daliban da aka yi.
Ya ce nan gaba idan za a sake yin wani kididdigan daliban ma’aikatar ilimi za ta gayyaci hukumar NYSC, NOA da hukumar kididdiga ta kasa.
“Ina da tabbacin cewa za a samu karin yawan dalibai a kididdigan da za a yi nan gaba domin yara idan sun ji cewa akwai abinci kyauta za su so na zuwa makaranta.
“Gwamnatin jihar Kano ta amfana matuka da wannan shirin ciyar da dalibai da gwamnatin tarayya ke yi domin duk wata gwamnatin taraya na aiko wa jihar Kano Naira biliyan 1.5.
Bayan haka kwamishinan ya ce an samu karuwa a yawan ma’aikatan dake girka wa daliban abinci daga 9,511 zuwa 12,258.
Jami’in shirin ciyar da yaran makarantar firamare na jihar, Baba Aminu-Zubairu yace jihar Kano ta fi samun yawan dalibai da suka koma makaranta duk da fama da aka yi da Korona.
Zubairu ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da su wayar da kan iyaye mahimmanci da alfanun da ke tattare da saka yaro a makaranta.