‘Yan sanda sun kama dillaliyar siyar da jarirai a Enugu

0

Rundunar ‘yan sanda jihar Enugu sun kama Blessing Eze mai shekara 27 da laifin killace wasu mata hudu masu ciki a gidanta.

Rundunar ‘yan sanda sun maka Blessing a kotu bisa laifin boye mata masu ciki a gidanta, safarar ‘yan mata da dillacin Jarirai.

Lauyan da ya shigar da karan B.I Ogbu ya ce a ranar 17 ga Yuni Blessing da wasu abokan aikinta da ‘yan sanda ke farauta suka boye wadannan mata masu ciki a gidan ta.

Blessing ta boye matan ne zuwa su haihu daga nan sai ta siyar da jariran a asibiti.

Blessing dai ta musanta aikata wadannan laifi da ake zarginta da aikatawa.

Bayan haka alkalin kotun J.N. Achi-Kanu ya bada belin Blessing akan Naira 500,000 tare da gabatar da mai bada shaida daya a kotun.

Za a ci gaba da Shari’a ranar 3 ga watan Agusta.

Share.

game da Author