Shugaban shirye-shirye na shirin ciyar da daliban makarantar firamare na gwamnatin tarayya dake jihar Cross Rivers Gab Okulaja ya koka kan yadda tsadar farashin abinci ke kawo wa shirin cikas a jihar.
Okulaja ya fadi haka ne ranar Litini a garin Calaba a hira da ta yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN.
Ya yi kira ga gwamnati da ta samo hanyoyin rage tsadar farashin abinci musamman yanzu da a dalilin wannan shiri yara ke kwararowa zuwa makarantun firamare a jihar.
“Babban matsalar mu shine yadda farashin abinci ya sama zuwa kashi 100% a kasar nan sannan har yanzu albashin masu girka abincin yaran makarantan bai karu ba tun da aka fara shirin a shekarar 2017.
“Kamata ya yi gwamnati ta Kara yawan kudaden da take kashewa kowani dalibai domin a rika dafa musu abinci mai kyau.
Bayan haka Okulaja ya kuma kara yin kira ga gwamnati da ta saka kananan yara da ake fara saka su a makaranta wato ‘Nursery’ a cikin Shirin.
A lissafe dai shirin ciyar da daliban makaranta na gwamnatin tarayya na ciyar da yaran makarantan firamare daga aji daya zuwa uku miliyan 9 a kasar nan.
A jihar Cross Rivers Shirin na ciyar da yaran makaranta 280,000 a makarantu 1000 dake fadin jihar.