Gwamnatin jihar Jigawa ta yi watsi da aikin ginin wani asibiti mai gado 250 da aka fara shi a ƙaramar hukumar Hadejia, shekaru biyar (5) da su ka wuce.
Tun da farko an baiwa kamfanin Philko kwangilar aikin ginin asibitin ne akan kuɗi kuɗi Naira Biliyan Ɗaya da Miliyan Ɗari Biyar, daga bisani aka sake duba kuɗin kwangilar inda aka mayar da ita Naira Biliyan Ɗaya da Miliyan Ɗari Takwas, kamar yadda daraktan bin diddigin ayyuka da gudanar da shi akan daidaitacciyar hanya na jihar Jigawa, Ado Husseini ya bayyana.
Menene Tarihin Kwangilar Ginin Asibitin?
An tsara aikin samar da asibitin ne da nufin ya zama asibiti mafi girma a masarautar Hadejia, wanda zai maye gurbin tsohon asibitin da firimiyan jihar Arewa marigayi Sa Ahmadu Bello ya gina shi a shekarar 1962.
Masarautar ta Hadejia ta ƙunshi ƙananan hukumomi guda takwas da su ka haɗa da ƙaramar hukumar Hadejia da Mallam Madori da Kaugama da Auyo da Kafin Hausa. Sauran sun haɗa da Kirikassamma da Birnawa da kuma Guri.
Tun da farko Gwamna Muhammad Badaru ya ƙaddamar da shirin kwangilar ginin asibitin ne a ranar 27 ga watan Disambar shekarar 2017, inda aka baiwa kamfanin Philko kwangilar akan kuɗi Naira Biliyan Ɗaya da Miliyan Ɗari Biyar, tare da baiwa kamfanin wa’adin watanni 18 wajen kammalawa.
A lokacin bikin ƙaddamarwar an jiyo Gwamna Badaru yana cewa “Za a gina wannan asibitin a cikin watanni 18 kacal, kuma kamfanin gine – gine na Philko ne ya samu nasarar samun kwangilar ginin asibitin bayan ya cika dukkanin wata ka’ida”
Ya ƙara da cewa “Wannan aikin shi ne irinsa na farko a faɗin jihar Jigawa, kuma hatta maƙotan jihohin irinsu Yobe da Bauchi da ma jamhuriyar Nijar za su amfana da asibitin idan aka kammala shi”
Haka kuma a gurin taron mai martaba Sarkin Hadejia, Abubakar Maje – Haruna ya bayyana farin cikinsa bisa kawo ginin asibitin zuwa masarautar sa. Ya ƙara da cewa “Wannan aiki da shi ne irinsa na farko da al’ummar masarautar Hadejia su ka shafe gomman shekaru suna mafarkin tabbatar sa”
Shekaru Biyar Da Watsi Da Aikin Ginin Asibitin
A cikin shekarar 2021 jaridar PREMIUM TIMES ta bi diddigin yadda aka yi watsi da aikin ginin asibitin, inda ta gano har yanzu a nan jiya – i – yau duk da wa’adin da gwamnan ya bayar na kammalawa akan lokaci a shekarar 2019.
Haka kuma PREMIUM TIMES HAUSA ta bi diddigin kasafin kuɗin jihar Jigawa, inda ta gano tsahon shekaru ba a iya saka kuɗin aikin ginin asibitin na Hadejia tare da wasu asibitocin da ake ginawa a ƙananan hukumomin Birnin Kudu da Kazaure
A kasafin kuɗin shekarar 2017 an amince a kashewa gini asibitocin Naira Biliyan Ɗaya da Miliyan Ɗari Biyu, sai dai iya kuɗin da aka saka domin yin aikin su ne Naira 377,297,299. Inda aka yi amfani da kuɗin wajen kammala aikin babban asibitin Birnin Kudu da cigaba da aikin ginin asibitin na Hadejia da kuma sanya tubalin ginin asibitin kwararru da ke Kazaure.
Haka kuma a kasafin kudin shekarar 2018 an ware Naira Miliyan 600 domin cigaba da aikin asibitin sai dai an fitar da Naira 745 997,586. Haka kuma a shekarar 2018 gwamnatin jihar ta kashe kuɗin da ya zargi wanda aka ƙayyade a kasafin kudin, inda ta kashe Naira 145,997,586, sai dai babu tabbacin ko majalisar dokokin jihar wacce ta ke ƴar amshin shatar gwamanatin jihar ta amince da fitar da kuɗin.
A kasafin kuɗin shekarar 2019, an ware kuɗin fiye da Naira Biliyan Ɗaya da Miliyan Ɗari Biyar domin ginin asibitoci uku, sai dai iya Naira 1, 380,170,420 aka fitar.
Hakazalika a ƙunshin bayanan kasafin kudin shekarar 2020 ya nuna cewa an warewa aikin ginin asibitin na Hadejia Naira miliyan 574. Sai dai a kasafin kuɗin shekarar 2021 an ware Naira Biliyan Ɗaya da Miliyan Ɗari Uku akan aikin ginin asibitoci uku. A cikin kuɗin har da aikin kashi na biyu na asibitocin.
Sai dai kamar lokutan baya, a yanzu abu ne mai wahala mutum ya samu cikakken bayani ko kuma bibiyar yadda tsarin kasafin kuɗin jihar ta Jigawa ya ke, wanda hakan ne zai sanya a yiwa gwannatin adalci kamar yadda wani ɗan jarida Ahmad Rufa’i ya bayyana.
“A mulkin soja kwamishinan kuɗi ne ke tara ƴan jarida da manema labarai ya yi musu bayanin abubuwan da kasafin ƙudi ya kunsa, amma shekaru shida a wannan gwamnatin an yi watsi da wannan ɗabi’ar wanda hakan ya kara ɗabi’ar cin hanci da rashawa” in ji ɗan jaridar.
Dan jaridar ya ƙara da cewa kamata ya yi gwamnati ta dinga gudanar da ayyukanta a buɗe ta yadda hakan zai gina gaskiya tsakanin waɗanda ake mulka da kuma shugabanni, kuma hakan ne zai sanya al’umma su gamsu cewa ana tafiyar da dukiyarsu ta hanyar da ya kamata.
Me Al’ummar Masarautar Hadejia Su Ke Cewa?
Shugaban ƙungiyar cigaban masarautar Hadejia wato Hadejia Emirate Development Association, (HEDA) Abdullahi Kafinta, ya ce sun rubuta ƙorafi akan yadda ɗan Kwangilar ke jan ƙafa akan aikin ginin asibitin tare da miƙa ƙorafinsu zuwa ga mutanen da abin ya shafa ciki har da Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar, amma babu wani mataki da aka ɗauka.
Abdullahi Kafinta ya ce babu wani aiki da gwamnati za ta gudanar da shi a masarautar Hadejia ba tare da kungiyarsu ta HEDA ta bibiye shi ba, tare kuma da wayar da kan al’ummar masarautar akan alfanun sanya ido dan ganin aikin ya kammala.
Ya ƙara da cewa amma akan batun yadda aka yi watsi da ginin asibitin kwararru na Hadejia, babu wanda zamu zarga sai gwamnatin jihar domin ita ta bayar da wa’adi kuma wa’adin ya daɗe da wucewa kuma mun rubutawa gwamnatin ƙorafi daban – daban domin jin dalilin da ya sanya aka yi watsi da aikin, amma shiru babu amsa.
“Watsar da aikin ginin asibitin da gwamnatin jihar Jigawa ta yi yana damun mu domin idan mu kalli yadda wa’adin zangon mulkin gwamanatin na biyu ya ke ƙarewa, kuma babbar damuwar al’ummar masarautar Hadejia ita ce gwamnatin Badaru ta ƙare ba tare da an ƙarasa ginin asibitin ba” In Abdullahi Kafinta
Haka kuma Abdullahi Kafinta ya ƙara da cewa mun rubutawa gwamnatin jihar Jigawa ƙorafi har kashi uku domin jin dalilan da ya sanya aka yi watsi da ginin asibitin amma shiru ka ke ji wai Malam ya ce Shirwa, wanda hakan ne ya sanya al’ummar masarautar Hadejia yanke ƙauna akan aikin.
Ya ce sakamakon rashin asibitin ƙwararru a yankin masarautar ta Hadejia, ya tilastawa al’ummar yankin zuwa maƙotan jihohi kamar su Kano da Yobe domin neman lafiya. Ya ce asibitin da ake da shi na gwamnati a yanki shi ne wanda Firimiyan jihar Arewa, Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto ya gina a shekarar 1962, wanda kuma ya yiwa al’ummar yankin kaɗan.
“Samar da asibitin kwararrun yana da matuƙar muhimmanci sai dai bamu gamsu da yadda ake tafiyar da aikin ba, domin mun bi diddigin yadda ake aiwatar da wasu ayyukan a wasu yankunan kuma tuni an kammalasu mutane sun fara amfana, amma me ya sa namu ya zama saniyar ware?” In ji Abdullahi Kafinta.
Ya ƙara da cewa a zabukan shekarun 2015 da 2019 al’ummar masarautar Hadejia sune su ka fi kowacce al’ummar masarauta kaɗawa gwamna Muhammad Badaru ƙuri’a, sai dai shiru bamu ga alfanun haka ba, domin gwamnatin ta yi watsi da mu”
Yadda aka bada kwangilar
Babban daraktan hukumar bin diddigin ayyuka da gudanar da shi akan daidaitacciyar hanya na jihar Jigawa, Ado Husseini ya musanta cewa babu gaskiya akan batun cewa wai an baiwa kamfanin da bai cancanta ba kwangilar ginin asibitin, ya ce hakan siyasa ce kawai da kuma hamayya daga ƴan adawa.
Ado Husseini ya ce tsarin kwangila yana tafiya ne tare da amincewa akan abin da ya ke cikin kasafin kudi, sannan kuma sai an bibiyi yadda aikin zai kasance kafin a amince da aikin. Kuma kwangilar asibitin kwararru na Hadejia shi ma sai da aka bi wannan bai zama na daban ba.
Haka kuma daraktan ya ce ayyukan ofishin bin diddigin na jihar Jigawa a buɗe ya ke babu wata ƙumbiya – ƙumbiya ko rashin gaskiya a dukkanin wani aiki da su ke gudanarwa, kuma suna ƙoƙarin wajen ganin an kammala dukkanin wani aiki akan darajar kuɗin da aka bayar domin a samu nagarta da ingancin aikin.
Ya ƙara da cewa tuntuni ya kamata a ce an kammala aikin ginin asibitin kwararru na Hadejia tare da ƙaddamar da shi amma ofishinsa ne ya ɗauki alhakin jan ƙafar da aikin ginin ya ke yi. ” Ofishin bin diddigin ayyuka shi ne silar da aikin kwangilar ke jan ƙafa tare da tafiyar hawainiya”
Ya ƙara da cewa “Babban burinmu ne mu ga an kammala aikin wannan asibiti tuntuni to sai dai an samu chanje – chanje a kwangilar ginin asibitin, domin da farko dai an sake fasalin taswirar ginin asibitin da kuma ƙoƙarin banbance gurin da aikin ginin asibitin zai dace, la’akari da irin yanayin ƙasar Hadejia”
“Da farko an bayar da kwangilar ginin asibitin ne akan kuɗi Naira Biliyan Ɗaya da Miliyan Ɗari Biyar, sai dai daga baya an sake duba fasalin kwangilar inda aka mayar da ita zuwa Naira Biliyan Ɗaya da Miliyan Ɗari Takwas, da nufin kammala kashin farko na ginin asibitin, kuma na tabbata yanzu haka an kammala aikin” In ji Ado Husseini.
Haka kuma babban daraktan ya ce wakilin da zai sanya daga ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, ya rubutawa ɗan kwangilar takarda inda ya bayyana damuwarsa akan yadda aka samu jan ƙafa wajen aikin. Ɗan kwangilar ya buƙaci a ƙara masa watanni biyar, amma duk da haka ya gaza gabatarwa da ma’aikatar lafiyar fasalin aikin duk da ƙarin watanni da ya buƙata kuma aka ba shi”
Amma a yanzun nan da mu ke magana da kai (Alhamis 27 ga watan Mayu), ofishin bin diddigin aikin ya rubutawa ɗan kwangilar takardar akan ya dawo bakin aikin.
Dalilan Da Ya Sanya Ba Zamu Soke Kwangilar Ba
Ado Husseini ya ce babban dalilin da ya sanya gwamnati ba za ta soke kwangilar ba shi ne ba zai taɓa amfanar da ɓangarorin biyu, kuma akwai buƙatar al’ummar masarautar ta Hadejia su ƙara haƙuri.
Soke kwangilar zai mayar da hannun agogo baya, domin za a ɗauki tsahon shekaru ba tare da an kammala aikin kuma an ƙaddamar da shi ba daga ɓangaren gwamnati ba. A dan haka dukkanin wanda abin ya shafa da su yi haƙuri akan lamarin.
Ɗan Kwangilar Ba Ya Binmu Bashi
Shugaban hukumar bin diddigin ayyukan na jihar Jigawa, ya ce fiye da shekara guda gwamnatin jihar ta biya dukkanin wasu ƴan kwangila kudadensu, dan haka babu wani kamfani ko ɗan kwangila da ya ke bin gwamati ko Sisin Kwabo
“Na birgi kirji tare da tabbatar maka da cewa babu wani ɗan kwangila da ya ke bin jihar Jigawa ko Sisin Kwabo. Mun kammala dukkanin biyan kuɗaɗen ƴan kwangila ƙasa da wata. A game da wannan kwangilar kuma ta ginin asibitin kwararru na Hadejia ina tabbatar maka da cewa babu sauran wani kuɗi da ba a biya ɗan kwangilar ba” In ji Ado Husseini
Lamarin Ya Fusata Gwamna Badaru Har Yayi Barazanar Gayyato Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Mai Zaman Kanta Ta ICPC A Cikin Lamarin
Wata majiya ta bayyana cewa batun aikin kwangilar ginin asibitin na Hadejia ya fusata Gwamna Badaru, lamarin da ya kai ga ya yi barazanar gayyato hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ƙasa ICPC, domin bincikar yadda aka yi watsi da kwangilar ta kasance.
Majiyar ta ƙara da cewa a maganar nan da mu ke da kai, Gwamna Badaru bai ji daɗin yadda aikin kwangilar ginin asibitin kwararru na Hadejia ba, musamman akan yadda su ka karya alkawari wanda hakan ya sanya ya samu ƙorafi daban-daban daga masarautar Hadejia, sai dai gwamnan ya gaza ɗaukar mataki sabdoa wanda aka danƙawa kwangilar abokin siyasar sa ne, wanda saboda wasu dalilai ba za a ambaci sunansa ba.
Hakazalika majiyar ta ce a ranar 7 ga watan Mayun shekarar nan, Gwamna Muhammad Badaru ya baiwa ofishin hukumar ICPC da ke Kano sabuwar Mota ƙirar Toyota Hilux, domin su samu karfin gwiwar bincikar yadda aikin kwangilar ya gudana.
A lokacin bayar da motar da gwamna Muhammad Badaru ya yi wanda ya samu wakilicin babban sakatare a ofishin sakataren gwamnatin jihar ta Jigawa, Ado Sadiq, ya bayyana cewa gwamnatin Jigawa, ta himmatu wajen yin koyi ga tsarin gwamnatin shugaba Muhammad Buhari, wajen ganin an bayar da dukkanin wata kwangila akan ka’ida da kuma doka da oda.
A nasa ɓangaren shugaban hukumar ta ICPC reshen jihar Kano, Umar Muhammad godewa gwamnan ya yi akan wannan gudummawar da ya baiwa ofishin na su, ya kuma sha alwashin yin amfani da motar yadda ya dace.
Ya ƙara da cewa hukumar ta ICPC za ta yi amfani da motar wajen bibiyar ayyukan da aka bayar a mazabu daban – daban da ke faɗin jihar.
Gwamnatin Jigawa Ta Himmatu Akan Aikin – Kakakin Gwamnati
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim Mamsa ya bayyana jaridar PREMIUM TIMES, gwamnatin jihar Jigawa ta himmatu wajen ganin an kammala ginin asibitin ƙwararrun na Hadejia akan lokaci, ya kuma buƙaci al’ummar masarautar da su ƙara haƙuri akan batun.
Bala Ibrahim Mamsa ya ce asibitin na Hadejia yana cikin manyan cibiyoyin lafiya da gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya mayar da hankali akai. Baya ga ginin asibitin na Hadejia, gwamnan ya yi alƙawarin gina karin wani asibitin a ƙaramar Kazaure ƙari kan na Hadejia.
Kwamishinan ya ƙara da cewa idan aka kammala ginin asibitin zai yi kafada da kafada da asibitin gwannatin tarayya da ke babban birnin jihar ta Jigawa.
“Muna tabbatarwa da al’ummar masarautar Hadejia cewa gwamnati ta himmatu wajen ganin an kammala aikin ginin asibitin ƙwararrun da ke yi” In Ji Bala Ibrahim Mamsa
Me Kamfanin Da Ya Ke Kwangilar Ya Ke Cewa Akan Batun?
Babban Injinyan da ke kula da aikin ginin asibitin Injiniya Habibu Aliyu da ya yi magana a madadin kamfanin na Philko ya shaidawa PREMIUM TIMES cewa babban dalilin da ya kawo tsaiko wajen aikin sun haɗa da yadda aka sake duba fasalin kwangilar da jinki wajen biyan kuɗi da kuma annobar cutar Korona da aka yi fama da ita.
“Bayan da kamfanin Philko ya buƙaci da a sake duba yanayin aikin kwangilar saboda yanayin ƙasar da za a yi aikin ba zai ɗauka ba, a nan ne gwamnati ta ɗauki tsahon watanni Takwai kafin ta bayar da amsa akan lamarin wanda hakan ne ya ƙara haifar da jinkirin aikin” In ji Habibu Aliyu
Injinya Habibu Aliyu ya ƙara da cewa wakilin ma’aikatar lafiya da zai sanya ido akan aikin bai sanar da gwamna Badaru cikakken bayani akan lamarin ba kuma haka ma a ɓangaren yadda aka sake duba fasalin kwangilar da kuma buƙatar biyan kuɗin sun ɗauki watanni uku (3) zuwa huɗu (4), wanda hakan ya sake haifar da jinkiri akan aikin.
A ƙarshe Injiniyan ya ce kamfanin na Philko zai iya kammala aikin ginin asibitin ne kawai idan har gwamnati ta sakar masa isassun kuɗi.