SHIRIN NOMAN RANI A KANO DA JIGAWA: Manoma Na Murna, Fulani Na Kuka

0

Taron buɗe gagarimin Shirin Bunƙasa Noman Rani a Kano da Jigawa, wanda Gwamnatin Tarayya ta damƙa wa manoman jihohin biyu filayen noman rani har hekta 289, ya wuce. Yayin da manoma ke murna da shirin, su kuma makiyayan yankin kuka cewa shirin noman ranin a ƙarƙashin Gari Irrigation Project ya tauye masu rayuwar sosai.

Makiyaya sun yi ta ƙorafin cewa aikin noman ranin ya toshe masu burtalolin da su ke bi su na kiwon shanun su.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda aka yi bikin damƙa filayen ga manoma, a Ƙaramar Hukumar Roni, Jihar Jigawa, a ranar Juma’ar da ta wuce.

Shirin zai bunƙasa noman rani, musamman noman shinkafa har tan 150,000 a kowace shekara, kamar yadda Gwamna Abubakar Badaru ya bayyana, idan aka haɗa da wadda ake nomawa a Haɗeja-Jama’are.

“A wannan shirin noman rani, manoma ba su buƙatar injin ban-ruwa da janareto, kuma dama su ne ke sa aikin noma yin tsada.” Inji Gwamna Badaru.

Asalin Shirin Noman Rani Na Gari Irrigation Project:

Asalin shirin dai an fara shi ne tun lokacin da Shugaba Buhari ke shugabancin Hukumar Tara Kuɗaɗen Man Fetur (PTF). Gwamnatocin da su ka biyo baya sun yi watsi da shirin. Sai yanzu ne aka farfaɗo da shirin.

A wurin taron, Gwamnatin Tarayya ta damƙa wa manoman Jigawa hekta 289

Gwamnatin Tarayya ta maida wa manoman Jigawa hekta 289 na gonakin noman rani a ƙarƙashin Shirin Gari Irrigation Project.

Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Harkokin Samar da Ruwa, Kenechukwu Offie ne ya bayyana haka, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Ministan Harkokin Noma, Suleiman Adamu ne ya damƙa masu filayen a ranar Juma’a, bayan kammala wani aikin noman rani da aka yi.

Sanarwar ta ƙara da cewa aƙalla manoma 1,472 ne za su amfana da shirin.

Shirin ya na a ƙarƙashin ƙudirin Shugaba Muhammadu Buhari na ganin an haɓaka tattalin arziki, wadatar abinci da kuma inganta walwalar ‘yan Najeriya.

Ya na a ƙarƙashin shirin ganin an fitar da mutum miliyan 100 daga ƙangin talauci a cikin shekaru 10.

Ya ce an sake farfaɗo da shirin ne bayan jinkirin sama da shekaru 20 da shirin ya tsaya cak.

Da ya ke jawabi, Minista Adamu ya ce shirin zai samar da hekta 2,114 waɗanda za a riƙa tura masu ruwa daga madatsar ruwa ta Da Marke da ke Arewa maso Gabas da Ƙunshi ta cikin Jihar Kano.

Aikin noman rani da magudanan ruwa da ma-aikatar ruwa ta gudanar, sun shafi garuruwan Kazaure, Roni a Jihar Jigawa. Sai kuma Ƙunchi, Ɗambatta da Makoɗa cikin Jihar Kano.

Sarkin Kazaure Najib Adamu ya yaba wannan gagarimin shiri, kuma ya roƙi jama’a kada su bari wannan dama da su ka samu ta shiririce masu.

An Kashe Mana Burtali Da Wuraren Kiwo -Sarkin Fulanin Roni:

Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah na Ƙaramar Hukumar Roni, ta Jihar Jigawa, Ayuba Shu’aibu, ya shaida wa manema labarai cewa ya yaba da aikin, amma kuma an toshe wa makikiya hanyar wucewa su je kiwo.

“Muna fatan gwamnati za ta duba kukan mu domin an tare wa makiyaya wurin kiwo da hanyoyin tafiya da shacnun wurin kiwo.

“Kai da ganin makiyaya ka san ba su yi murna ba, domin manoma ne kaɗai ke murna banda makiyaya. Mu makiyaya ba gamsu da yadda aka yi tsarin ba.” Inji shi.

Ya ce tun farko akwai burtalolin shanu, amma da aka zo wurin aiki, sai aka laƙume wuraren kiwon mu da burtalolin domin a daɗaɗa wa manoma.”

Adamu Ibrahim daga Ƙunchi da Umar Ado daga Ƙaramar Hukumar Makoɗa, su na Fulani ne kuma koken su iri ɗaya da na Shu’aubu, Shugaban Miyetti Allah na Roni.

Sai dai kuma Babban Sakataren Hukumar Kula da Makiyaya da Manoma ta Jihar Jigawa, Rabiu Miko ya ce a ko da yaushe Gwamnati na keɓe burtalolin makiyaya. Don haka wannan aikin ma bai karya ƙa’idar ba.

Sai dai kuma Manoma irin su Usman Mu’azu daga Makoɗa, ya ce tuni har manoma sun fara girbe albasa, tumarir, masara, shinkafa da sauran kayan abinci da kayan marmari a na su gonakin da aka damƙa musu.

Shi ma Isyaka Abubakar daga Ƙunchi ta Jihar Kano, ya ce aikin ci gaba ne daga muhimman ayyukan inganta rayuwa da Shugaba Buhari ke aiwatarwa. “Domin ba zan manta ba lokacin da ya na Hukumar PTF har nan ya zo ya duba aikin madatsar ruwan.”

Manoman sun kuma gode wa gwamnonin Kano da Jigawa.

Share.

game da Author