Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahdi Ali Gusau ya ce ba zai amsa gayyatar majalisar dokokin jihar ba saboda ya maka majalisar a kotu.
Idan ba a manta ba majalisar jihar ta gayyaci mataimakin gwamna Mahdi ya bayyana a gabanta ne saboda wai ya gudanar da gangamin siyasa a daidai ana jimamin rasuwar wasu mutane wanda ‘yan bindiga suka kashe a jihar.
A wata takarda da mataimakin gwamnan ya fitar ranar Alhamis, ya ce ba zai yiwu ya bayyana a gaban majalisar ba saboda maganar na gaban kotu.
” Idan na bayyana a gaban majalisa zai zama karya doka, domin kotu da kanta ta umarci majalisar ta dakata tukunna har sai ta gama nazari akan karar sannan ta yanke hukunci.
Tun bayan canja sheka da gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle yayi, ake ta kai ruwa rana tsakanin sa da mataimakin gwamnan jihar.
Ko da ya ke har yanzu ba su fito fili sun yi sa’insa a tsakanin su ba, Mahdi ya ce ba zai bi gwamna Matawalle APC.