Shekaru biyu tun ba a yi nisa da yin amfani da salon kamfen ɗin ‘O to ge’ aka ruguza gidan siyasar tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, daga sama har ƙasa a Jihar Kwara, tun ba a yi nisa ba har gayyar ta watse, zaratan da su ka ga bayan Saraki sun juya su na yaƙar junan su da makaman da su ka yaƙi Saraki da su.
Gidan Siyasar Saraki dai ya kafu ne tun zamanin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa na zamanin Jamhuriya ta Biyu, Olusola Saraki, mahaifin Bukola da Gbemisola Saraki.
Bayan Bukola Saraki ya yi Gwamna shekaru takwas, ya ɗora Abdulfatah Ahmed, wanda ya yi shekaru huɗu na farko a ƙarƙashin PDP.
Bayan kafa nPDP, ya bi Saraki sun koma APC, inda a can ma ya sake lashe zaɓe ya shekara huɗu.
To sai dai kuma gangamin ‘O to ge’ a lokacin zaɓen 2019 da aka yi domin kawo ƙarshen siyasar gidan Saraki, ya yi nasara.
Nasarar farko dai wanda APC ta tsaida takarar gwamna a Kwara shi ya yi nasara, wato AbdulRahman Abdulrazaq.
Nasara ta biyu kuma Saraki da duk waɗanda su ka fito takara a ƙarƙashin tutar sa sun ci ƙasa ba su yi nasara ba.
Gungun Ruguza Gidan Siyasar Saraki:
Wannan gungu sun haɗa da ‘Legacy Group’, wanda ya ƙunshi Gbemisola Saraki, ƙanwar Bukola Saraki, wadda ba su ga-maciji. Ita ce bayan nasarar zaɓen 2019 aka naɗa ta Ƙaramar Ministar Sufuri.
Akwai kuma gungun AA Group, wato Gwamna a yanzu wanda shi gungun mayaƙan su ka tsayar takarar gwamna, kuma ya yi nasara.
Akwai irin su Ministan Yaɗa Labarai, Lai Mohammed, wasu ɗaiɗaiku irin shugaban jam’iyyar a APC na lokacin, Bashir Bolarinwa.
Yadda Aka Fara Kitso Da Kwarkwata A Cikin Kai:
Tun a wurin zaɓen fidda gwani aka fara samun tangarɗa, inda a bisa kuskure aka soke ‘yan takara biyu, Salihu Mustapha da Mashood Mustapha.
Sai da ta kai uwar jam’iyyar APC ta ƙasa sun ba su haƙuri dangane da abin da aka yi masu. Duk da wasu na ganin cewa tuggu ne aka ƙulla masu, amma dai sun haƙura ba su kai ƙara ba.
Dawowa Rakiyar Gwamna Watanni Shida Bayan Zaɓe:
An shafe watanni shida kafin Gwamnan Kwara A.A ya naɗa kwamiahinoni. Hakan kuwa ya ɓata wa da dama gaggan APC na Kwara rai.
An samu saɓani da cukumurɗar tuggu da kutunguilar siyasa, har ta kai an tsige Shugaban Jam’iyya Bashir Bolarinwa. An yi zargin da hannun Gwamna aka kori Bolarinwa daga shugabancin APC a Kwara.
Shugaban Kwamitin Riƙon APC, Mai Mala-Buni ya naɗa Abdullahi Samari shugabancin rikon APC a Kwara bayan tsige Bolarinwa.
Tsige naɗa Borarinwa da naɗa Abdullahi Samari, ya fasa jam’iyyar APC gida biyu a Jihar Kwara. Akwai masu goyon bayan Gwamna, akwai kuma waɗanda ba su goyon bayan sa.
Rigimar Gwamna Da Minista Lai Mohammed:
Alaƙa ta yi tsami tsakanin Gwamna da Minista Lai Mohammed a lokacin sabunta rajistar ‘ya’yan jam’iyyar APC, inda Lai Mohammed ya ce “iya-shege” aka yi ba sabunta rajista ba.
PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin yadda Gwamnan Kwara ya tashi da katinan rajistar ‘yan jam’iyya sama, ya bar Lai Mohammed ya na susar ƙeya.”
Minista Lai a lokacin ya kira taron manema labarai a garin su Oro, inda ya nemi a sake sabunta rajista a jihar Kwara, domin Gwamna ya kwashe katin rajista ya raba wa magoya bayan sa.
Lai ya yi zargin cewa ba a bi tsarin da jam’iyyar APC ta gindaya wajen sabunta rajista ba.
Wakilin mu ya tabbatar da wani zargi da Lai Mohammed ya yi, inda ya ce ba a yi amfani da littafin rajistar mambobi ba, sai aka yi amfani da fallayen takardu, waɗanda hatta shi kan sa gwamnan ma da mutanen sa duk a fallayen farar takarda aka yi rajistar sunayen su.
Tuni dai wannan gayya ta watse kowa ya kama gaban sa. Jama’a da dama na ganin idan Saraki ya sake yunƙurawa a zaɓen 2023, zai dawo da martabar gidan siyasar Saraki daram.