Ba ni da ra’ayin takarar shugaban kasa, lokacin da aka zabe ni gwamnan Kaduna gashin kai na baki wul yanzu duk furfura – El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa bashi da wani ra’ayi ko shirin fitowa takarar shugabancin kasar nan domin na gwamna ma da ya ke kai yanzu ba karamin aiki bane.

El-Rufai ya kara da cewa a shekarun sa yanzu kamata yayi ya ɗan ɗaga kafa domin ofishin shugaban kasa ba wasa bane.

Gwamnan ya faɗi haka da wasu amsoshin wasu tambayoyi Tashar BBC Pidgin ta yi masa a hira da yayi da Helen na tashar a ofishin s

” Shugabancin Najeriya ba wasa bane. Ni yanzu ba shine a gaba na ba. Gwamna ma da na ke kai yanzu abin ba sauki. Lokacin da aka zaɓe ni gashin kai na baƙi wul amma yanzu duk kaina sai furfura saboda faɗi tashin aikin gwamna.

Da aka tambayeshi game da damke gogarman kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, El-Rufa’i ya ce hakan yayi daidai.

” Nnamdi Kanu ya tsallake beli, ya waske. Sannan kuma ko a inda yake bai ja bakin sa ya yi shiru ba, ya rika ingiza mabiyansa suna tada husuma a yankin kudu maso gabas da kuma kai hare-hare ga jami’an tsaro da ofisoshin gwamnati.

” Idan da Alkali ya so da an kama wanda ya tsaya masa sanata Abaribe. Da an ɗaure shi har sai Kanun ya bayyana.

Game da shirin sake zanga-zanga da kungiyar kwadago ke shirin yi a jihar a karo na biyu, El-Rufai ya ce yana nan ya na jiran kungiyar kwadagon.

” Su zo Kaduna su gani. Wannan karon ba za su sha da daɗi ba. Muna nan muna musu shiri.

Share.

game da Author