Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Tashoshin Talabijin ta Ƙasa (NBC), ta bayyana cewa irin yadda ake yaɗa labarai na matsalolin tsaron ƙasar nan ya na shafar jami’an tsaron da ke kan ayyukan daƙile matsalar tsaro.
A cikin wata takardar da NBC ta raba wa gidajen radiyo da talabijin ɗin, ta ce “tabbas aika labarai da sanar wa al’mma yanayin tsaron ƙasar su abu ne da ya wajaba a kan kafafen yaɗa labarai, to kuma akwai buƙatar a riƙa isar da saƙonnin a cikin taka-tsantsan.”
Sanarwar ta ƙara da cewa waɗansu bayanan su na da nasaba da ƙabilancin da ake alaƙantawa da su, hakan na haɗa ƙiyayya, nukura, gaba da nifaƙa tsakanin ɓangarori ko ƙabilu.”
Wasiƙar dai an rubuta ta ne a ranar 7 Ga Yuli, kuma Daraktan Sa-ido kan Labarai, Francis Aiyetan ne ya sa mata hannu a madadin Babban Daraktan NBC.
NBC ta ce kafafen yaɗa labarai kada su maida hankali wajen ƙara zugugutawa ko ruruta labaran da su ka shafi mayaƙan sunƙuru, Boko Haram, ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda.”
Wasiƙar kuma ta umarci kafafen yaɗa labarai su daina bai wa baƙin da su ka gayyato masa yin sharhi fili su na kalaman da ke ƙara ruruta ƙiyayya tsakanin ɓangarorin ƙasar nan.
Sannan kuma ta yi kira su daina bayyana sunaye ko munin irin ɓarnar da aka yi wa jami’an tsaro, domin hakan na damun su kuma ya na taɓa tunanin su.
NBC ta runatar da su Ka’idojin Doka ta Sashe na 5.41(f) da ta 5.4.3 na Dokar NBC.
Wannan wasiƙa ta zo daidai lokacin da ake ƙorafin Gwamnatin Buhari na ƙoƙarin ƙaƙaba wa kafafen yaɗa labarai takunkumi irin wanda ya yi a lokacin da ya ke shugaba na mulkin soja.
Haka kuma ana ci gaba da nuna damuwar cewa gwamnati ta fitar da wannan wasiƙa ce ganin yadda ake yawan tsangwamar ta cewa ba ta yin abin a-zo-a-gani sosai wajen daƙile tsaro.