Gwamnatin Najeriya ba ta bada kwanaki Uku, hutun Babban Sallah ba – Binciken DUBAWA

0

Eid-ul-Adha wato Babban Sallar kamar yadda ake yi masa lakabi da a kasar Hausa, na daya daga cikin bukukuwa masu mahimmanci ga musulmai a ko’ina a fadin duniya da kasar Najeriya da al’ummar musulmi ke da yawan gaske.

Sai dai al’ummar musulmin na amfani da kwanakin watan Hijra ne wajen tsayar da ranar yin bukukuwan Sallar wanda kuma ba koda yaushe bane yake kasancewa daidai da kwanan watan nasara. Don haka, musulmi duk inda suke suna amfani da wannan kwanan wata na Hijira sannan kuma su jira sanarwar ranar gudanar da bukin mai mahimmanci daga bakin jagororin addinin a kasar.

A Najeriya Sarkin Musulmi, wanda kuma shi ne shugaban majalisar kolin musulmin Najeriya (NSCIA) Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bayyana ranar talata 20 ga watan Yuli 2021 a matsayin ranar da za’a gudanar da bukuwan Eid-ul-Adhan bana, wanda ya zo daidai da 10 ga watan Dhul-Hijja (1442AH). Shi ya sa ma Musulmai da ma sauran ‘yan Najeriya ke sauraron gwamnati ta bayyana yawan ranakun hutun da zata bayar don shagulgulan wannan rana.

Da ma kuma Gwamnatain Tarayya ta saba bayar da hutun kwanaki biyu lokacin sallah. Musulmin Najeriya musamman wadanda sukan yi tafiya mai nisa lokacin bukin sukan yi korafin karancin kwanaki. Wata kila shi ya sa mutane suka rika yada labarin cewa gwamnati ta bada hutun kwanaki uku maimakon kwanaki biyu da ta saba abyara wa.

Tantancewa

Dubawa ta sami sakon da aka ce an yada shi a manhajan whatsApp sau da yawa, wanda ke cewa gwamnatin tarayyar ta bayyana ranakun 20, 21 da 22 na watan Yuli a matsayin ranakun hutun bukin sallar Eid-ul-Adha. Dubawa ta fara bincike da bin mafarin labarin wanda ke nuna cewa wata jarida mai suna Western Daily News ta wallafa labarin.

Sai dai a maimakon ganin cikakken labarin a shafin jaridar, mun rika ganin sakon da ke cewa akwai matsala da shafin da muke nema, sannan ba abin da ke nunawa a shafin.

Mun kuma sake duba shafukan gwamnatin tarayyar da ke kafofin sadarwa na soshiyal midiya, a nan ma bamu ga wani sako makamancin wanda ake yayadawa ba.

Martanin gwanmati

Dubawa ta tuntubi ma’aikatar harkokin cikin gida kuma jami’an da suka tattauna da mu bisa sharaɗin ba za mu bayyana sunayen su ba (tunda ba a basu izinin magana a hukumance ba) sun ce sakon ba gaskiya ba ne, ma’aikatar za ta shaida ranakun da ya kamata daga baya kuma zasu kasance ranakun 20 da 21 na watan Yuli 2021.

A Karshe

Sakon da ke cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana ranaku uku a watan Yuli a matsayin hutun sallah karya ne.

Share.

game da Author