Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa mutum 203 sun kamu da cutar korona kuma mutum daya ya mutu a Najeriya ranar Lahadi.
Wannan shine karon farko da kasar nan ta samu mutanen da suka kai yawan haka tun 31 ga Mayu.
Bisa ga sakamakon gwajin an gano wadannan mutane a jihohi 6 da Abuja ne.
Alkaluman da aka fitar ranar Lahadi ya nuna jihar Legas ta fi yawan mutanen da suka kamu da cutar inda suke mutum – 186, Edo-4, Oyo-4, Rivers-4, Kwara-2 da Abuja-2.
Zuwa yanzu mutum 169,532 ne suka kamu, mutum 2,127 sun mutu.
An sallami mutum 164,699 sannan mutum sama da 2,000 na killace a asibitocin kula da masu fama da cutar.
An yi wa mutum miliyan 2.3 gwajin cutar daga cikin mutum miliyan 200 din dake zama a kasar nan.
A lissafe dai mutum 963 ne suka kamu a cikin wannan mako inda akalla mutum 136 ne ke kamuwa da cutar a rana.
Najeriya ta fara samun karuwa a yaduwar cutar tun bayan bayyanar Korona nau’in Delta.
Masana sun ce ita nau’in Korona ta Delta, ta na da saurin kama mutum sannan tana da wahalar warkewa. Idan har mutum ya kamu da ita ya kan yi fama da ita na tsawon lokaci.
A dalilin haka yake da mahimmanci a ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar musamman a wannan lokacin na sallah laiya.