Abubakar Isma’il malamin firamare ne a Kano. Shi kuma Opeyemi Adeyemi ma’aikacin wani kamfani ne a Obalende, cikin Legas. Su biyun kukan su iri ɗaya dangane da masifar tsadar rayuwar da ake ciki.
“A wannan matsanancin halin, wanda aka rage wa albashi sai ya yi murna kawai, tunda ba korar sa aka yi ba ɗungurugun.
“To ni ba kora ta aka yi ba, albashi na aka zaftare. Wannan ibtila’i da ya same ni, ya canja rayuwa ta da ta iyali na. Saboda a yanzu haka abincin rana gagara ta ya ke yi, sai dai na riƙa ‘yan kame-kame.
“Ko dai na ci gasasshiya ko dafaffiyar masara da rana, na kwankwaɗi ruwa, ko kuma na jiƙa gari da ruwa da sukari na sha, na saurari jiran abincin dare.” Inji Adeyemi, wanda ya ƙara da cewa:
“Kuɗin wutar lantarki na neman gagara ta. Sauƙi na ma ba ni da yara ƙanana da yawa, amma da sai kuɗin makarantar yara sun gagare ni biya.”
Kamar Adeyemi kamar Isma’il, malamin firamaren da ya ce, “ai ni rabo na da sayen ƙaramin buhun shinkafa tun kafin Buhari ya hau mulki.”
Malamin ya ce a yanzu kafin ka ga gidan talakan da ake yin abinci da jar miya, sai wane-da-wane. Saboda kayan miya sun yi tsada kamar wasu kayan alfarma.”
Isma’il ya ce ba ya iya sayen kwanon wake saboda yanzu ya kai naira 1,600. Masara da gero da dawa waɗanda talaka ne ke noma su, a yanzu ko sunan su talaka ya ji wallahi sai hankalin sa ya tashi.”
Matsalar da Adeyemi da Ismail su ka shiga, irin ta ce miliyoyin ‘yan Najeriya da dama ke ciki a halin yanzu.
Bincike ya nuna a kullum kayan masarufi da kayan abinci su na tashi. Abin da ake sayarwa a kasuwannin birnin, ba daidai farashin sa yake da kasuwannin ƙauyuka masu ci sati-sati ba.
“Abin damuwar a kullum shi ne yadda farashin ke tashi a kowace kasuwanni. Abin da ka sani naira 500, idan ka koma wani sati naira 700 za a ce maka.”
Dalilan Tsadar Rayuwa Ga Talakan Najeriya:
Ɓullar cutar korona a ranar 27 Ga Janairu, 2020: Hakan ya tsayar da komai a ƙasar nan, ya karya tattalin arziki, miliyoyin ‘yan Najeriya sun talauce yayin da aka ƙaƙaba kullen korona.
Ƙarfin Tattalin Arzikin Cikin Gida Ya Samu Tawaya: Saboda masana’antu sun daina aiki. Babu kayan da ake sassafawa a cikin gida ana fitarwa a waje.
Sannan kuma masu aiki a masana’antu sun tagayyara, saboda an tilasta masu zaman gida.
Tarzomar #EndSARS: Wannan tarzoma ta haifar da kashe-kashe da asarar dukiyoyi masu ɗimbin yawa.
Dakatar da kai abinci a jihohin kudu da aka yi na wani lokaci ya haddasa masifar tsadar kayan abinci a kudancin ƙasar nan.
Matsalar Tsaro: Wannan babbar matsala ta haddasa tsadar rayuwa a Arewa, domin yankuna da dama noma ya gagara. Sannan kuma wasu kasuwannin yankunan karkara sun daina ci. Dama a irin waɗannan kasuwanni ake samun amfanin gona da arha, ana kaiwa cikin birane da garuruwa ana sayarwa.
Ƙarshen makon da ya gabata PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda yadda buhun garin kwaki ya tsere wa talaka fintinkau.
Garin rogo, wanda a ƙasar Hausa aka fi sani da garin kwaki, ya na ɗaya daga cikin abincin da duk wanda a shekarun baya aka ga ya daddage ya na ƙasumar sa, to ana danganta shi da talauci ko ƙarancin wadatar aljihu ko ta abinci a gida.
Amma a yau, duk da ɗimbin kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke kashewa wajen bunƙasa noma, hakan bai hana garin kwaki fecewa a guje ba, ya bi sahun sauran kayan abincin da ake nomawa a gida wajen tsula tsadar tsiya.
Kamar yadda shinkafa, wake, masara, gero da dawa su ke neman su gagari talaka, tuni shi garin rogo ya shige gaban su wajen tsada. Ya tsere wa gero da dawa da masara. Kuma ya yi wa talaka fintinkau, sai gani sai hange daga nesa.
Buhun garin kwaki mai nauyin kilo 100, wanda a shekarun baya ake sayarwa naira 16,000, yanzu idan ba ka da naira 40,000 ba za ta ka iya sayen sa ba a jihohi irin su Cross River, inda ake ganin kamar can ne ma ya fi arha takyaf.
Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna dalilai da dama da su ka haddasa ko da talaka ya iya sayen garin kwaki domin ya ci, to ba zai iya yi masa cin a ci a ƙoshi ba, irin wanda a shekarun baya ake tasa taiba a gaba ana ci har ciki ya cika.
Miliyoyin ma’aikatan da su ka ƙunshi na gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi waɗanda albashin su bai kai naira 40,000 ba, ba su iya cin garin kwaki su ƙoshi su da iyalan su. Sai dai a yi cin daga-bana-sai-baɗi, wanda ake yi ranar da aka ɗauki albashi.
Maciya tuwon alabo, wanda ake yi da rogo, su ma yanzu sai gani sai hange, ba kowa ke iya buɗe ciki ya danƙari tuwon alabo ba, duk kuwa da sulɓin ta lomar tuwon ke da shi. Saboda ba ta da sulɓi a cikin aljihun talaka.
A Najeriya dai batun tsadar abinci kullum sai hauhawa ya ke yi, ya ƙi saukowa ko gsngarowa ko kuma mirginowa a ƙasa.
A ƙididdigar da Hukumar Ƙididigar Alƙaluman Bayanai ta Kasa ta yi a watan Afrilu, ta nuna cewa cikin watan Maris, 2021 kayan abinci a Najeriya sun yi tsadar da ba su taɓa yi a tsawon shekaru huɗu da su ka gabata ba.
Garin kwaki wanda shi ne aka fi nomawa na biyu daga masara a ƙasar nan, a yanzu bincike ya nuna wanda ake nomawa ɗin ba ya wadata.
Manoma irin su Grace Ebit da wasu masana sun danganta matsalar da rashin nahartaccen tsari da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa, rashin kyakkyawan tsarin noma, rashin jari ko rashin lamuni daga gwamnati da kuma ƙarancin taki.
Masana sun ce kafin rogo ya sake yin arha a Najeriya, sai an dasa aƙalla metrik tan miliyan 28.3 a filin gonakin da aƙalla sun kai faɗin hekta miliyan 1.2.
Cikin watan Mayu PREMIUM TIMES HAUSA ta yi tsakuren yadda wake ya fi ƙarfin tukunyar girkin manoman da ke noma shi.