Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa an samu karin mutum 238 da suka kamu ranar yawon Sallah a Najeriya, mutum biyu sun rasu.
Alkaluman da aka fitar na ranar Laraba ya nuna cewa mutum 181 sun kamu a jihar Legas, Akwa-ibom-45, Oyo-8, Ogun-8, Ekiti-2 da Abuja-2.
Zuwa yanzu mutum 170,122 suka kamu da cutar sannan mutum 2,130 sun mutu a Najeriya.
An sallami mutum 164,741 kuma mutum 3,240 na killace.
Ga dukkan alamu korona na ci gaba da yaduwa a kasar nan musamman tun farkon wannan wata.
A dalilin haka ne NCDC ta yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da domin samun kariya.
Hukumar ta yi wannan gargaddi bayan da aka samu tabbacin bullowar zazzafar nau’in cutar ‘Delta’ a kasar nan.
Zuwa yanzu an yi wa mutum miliyan 2.4 gwajin cutar a kasar nan.
Idan ba a manta a wannan mako ne gwamnatin Najeriya ta bayyana shirin ko-ta-kwanan ɓarkewar sabuwar zazzafar cutar korona samfur ta uku, mai suna ‘Delta’ a jihohin Kano, Lagos, Ribas, Oyo, Kaduna da Filato da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
Gwamnati ta yi haka ne saboda ana yawan samun ɓulla da fantsamar launin korona mai zafin nan da ake kira ‘Delta’.
An gargaɗi jama’ar ƙasar nan kada su yi wasa ko sakaci, domin ita wannan samfur ɗin ‘Korona Delta’, lahira kusa ce.
Gwamnati ta kuma umarci dukkan jihohi su gaggauta shiri da kimtsin ɗaukar ƙwararan matakai, fiye ma da wanda aka ɗauka a farkon ɓarkewar korona.