ZABGE MA’AIKATA: El-Rufai ya warware wa Buhari zare da abawa, zai kafa wa NLC Kwamitin Bincike

0

Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya yi tattali har Fadar Shugaba Muhammadu Buhari ya warware masa duk wani kiki-kaka da zare da abawar da ke tattare da zabtare ma’aikatan jihar da ya ke kan yi.

Sannan kuma gwamnan na Kaduna ya ce zai tantsnce tsaki daga tsakuwa a kan zanga-zangar Shugabannin Ƙungiyar Ƙwadago na Ƙasa da su ka gudanar a Kaduna, cikin watan Mayu, 2021.

Ya ƙara da cewa a yanzu haka gwamnatin sa za ta ɗauki hayar da ma’aikatan wucin-gadi mutum 10,000.

“Saboda duk inda aka kori ma’aikata, to kuma ana buƙatar ƙwararrun da za su maye gurbin su..

“Shi ya sa za mu ɗauki hayar ma’aikata ƙwararru da su ka haɗa da malamai, likitoci, nas-nas da sauran ƙwararrun wasu fannoni daban-daban.”

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na El-Rufai, mai suna Muyiwa Adekeye ya sa wa hannu, Gwamna ya ce Gwamnatin Jihar Kaduna ta sha alwashin cewa ba za a sake maimaita abin da Ƙungiyar Ƙwadago ta Kasa ta haddasa wa jama’a ƙunci, takura, asara da tauye masu ‘yancin su ba.”

Adekeye ya ce duk wani abu da aka cimma a tattaunawar da wakilan Jihar Kaduna suka yi da Ƙungiyar Ƙwadago da Ministan Ƙwadago Chris Ngige, a ranar 20 Ga Mayu, zai buƙaci amincewar Majalisar Zartaswar Jihar Kaduna tukunna.

Tuni ya ce Gwamnatin Jihar Kaduna ɗin ta shaida wa Ministan Ƙwadago cewa ba za ta iya amincewa da yarjejeniyar da aka cimma ba ”

“Gwamnatin Kaduna ta ƙi amincewa a ce wai don an maida wani ma’aikaci ɗaya Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari a ce wai bi-ta-da-ƙulli aka yi masa, sai ka ce sauran ma’aikatan da ke Birnin Gwari su ba mutane ba ne.”

Share.

game da Author