Gwamnan Bauchi ya kori dukkan kwamishinonin sa

0

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed, ya sauke dukkan kwamishinonin sa baki daya.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai, Muktar Gidado ya shaida aika wa jaridu a ranar Laraba, ya bayyana sallamar “dukkan Kwamishinoni tare da rushe Majalisar Zartaswar Jihar Bauchi da sauran masu rike da mukaman siyasa da su ka hada da Sakataren Gwamnati, Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, har da dukkan Mashawartan Musamman.”

Sanarwar ta “tsame sunayen mutum hudu wadanda sallamar ba ta shafa ba.”

Babu dai wani dalilin sallamar a cikin sanarwar wadda ta hada da cewa kowane kwamishina ya damka harkokin ofis a hannun Babban Sakataren Ma’aikatar sa.

Bala Mohammed wanda dan jam’iyyar APC ne, ya gode wa dukkan wadanda ya sallamar.

Share.

game da Author