Gwamnan Jihar Jigawa ya karyata jita-jitannda ya karaɗe jihar wai ya tsige Auwalu Sankara, wanda daya ne daga cikin jadimansa.
” Awwal Sankara na nan a matsayinsa na Babban Mataimaki na musamman akan sabbin kafafen sadarwa, ga gwamna Badaru.
Tabbacin hakan ya biyo bayan jita jitan da ake yadawa bayan nadin sabbin makamai da gwamna Badaru yayi a jiya Talata.
PREMIUM TIMES ta rawaito yadda gwamna Badaru ya nada Habibu Kila da Ahmad Danyaro, a matsayin hadimansa na yada labarai.
Amma daga baya, gwamna Badaru ya shaidawa gidan radio Jigawa cewa, akwai kuskure wajen sanarwar inda yace Sankara yana nan daram a matsayinsa na mataimaki na musamman akan sabbin fafafen sadarwa.
Dukkanin hadiman zasuyi aiki tare da juna domin cigaban jihar ta Jigawa inji sanarwar.
Sankara shi ne ya rike dukkanin ofishoshin mai bawa gwamna shawara kan harkar yada labarai na tsawon fiye da shekaru biyu na wa’adi na biyu na gwamna Badaru.
Kafin daga bisani gwamna Badaru ya nada Yusuf Babura a matsayin maitaimaka masa akan harkar radio sai kuma nada Kila da Danyaro a ranar Talata.