Za a kashe wa EFCC naira miliyan 805.7 domin inganta tsaro a hedikwatar hukumar

0

Majalisar Zartaswa za ta kashe naira miliyan 806.7 wajen sayo kayan aikin inganta tsaro a hedikwatar Hukumar EFCC da ke Abuja.

Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ne ya bayyana wa manema labarai haka, a Fadar Shugaban Kasa.

Hakan ya biyo bayan tashi daga taron Majalisar Zartaswa na ranar Laraba a Fadar Villa, wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya jagoranta.

“Idan za ku iya tunawa daga 2011 an sha kai wa hukumomin gwamnati hari, har ma da ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja sai da aka kai wa hari.” Inji Lai.

“Saboda wadannan hare-hare da aka rika kaiwa a 2011, 2014 da 2018, sai Gwamnatin Tarayya ta kafa Kwamitin Tantance Hukumomin da ke Fuskantar Barazanar Tsaro, domin a inganta tsaron wadannan ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomi.

“A dalilin haka ne a yau EFCC ta gabatar wa Majalisar Zartaswa uzirin neman amincewa a kashe kudi a sayo na’urori hudu masu hana rumbunan tara bayanai rushewa. Kuma za a sayo sauran na’urorin kwafa da kwasar bayanai domin killace su, gudun kada rumbun ajiyar ya rushe.”

Sannan za a sayo waya mai tsawon mita 900 domin kewaye harabar ginin, sai na’urorin ganin abin da mutum ya ke dauke idan zai shiga hukumar EFCC, sai na’urorin binciken jakunkuna da na gano bama-baman da aka kimshe a cikin kaya.

Lai ya ce an kuma amince a sayo wa Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnati (FCSC) motoci guda 16.

Share.

game da Author