Majalisar Zartaswa ta amince a kashe naira biliyan 8.8 domin kammala aikin noman rani a Karamar Hukumar Bagwai ta Jihar Kano da kuma aikin samar da ruwa a Karamar Hukumar Biu ta Jihar Barno.
Ministan Harkokin Samar da Ruwa, Sulaiman Adamu ya shaida wa manema labarai bayan kammala taro a Fadar Shugaban Kasa cewa, aikin inganta noman rani na Karamar Hukumar Bagwai ta Jihar Kano ya tsaya cak ne saboda rashin kudin ci gaba da aiki.
“A yau na gabatar da bukatu biyu wadanda kuma duk gwamnatin tarayya ta amince da su. Na farko batun karasa aikin ruwan noman rani ne a Karamar Hukumar Bagwai ta Jihar Kano, wanda za a karasa a ‘Watari Dam’, wanda aka amince za a kashe wa naira biliyan 3.76.
“To aikin kwangilar ya yi nisa, har zuwa lokacin da ya tsaya cak saboda rashin kudi.
“Kamfanin Dantata and Sawoe ne aka bai wa kwangilar, tun cikin 2006 a kan yarjejeniyar kammalawa cikin shekaru biyu.
“Tun farko an amince za a yi aikin samar da filin noman rani ne mai fadin hekta 872.
“Mun yi bincike da bin-diddigi tun ma kafin na zama Ministan Ruwa aka fara binciken. Da na hau cikin 2015 mu ka kara tantancewa tare da bayar da muhimmancin ganin an kammala aikin, wanda aka yi watsi da shi a baya.
“Saboda haka yanzu dai majalisa ta amince a kara narka naira biliyan 3.763, ta yadda a yanzu aikin kwangilar zai kai naira biliyan 9.2, daga naira biliyan 5.4 na ainihin kudin kwangilar na farko. An hada har da kashi 7.5 na harajin VAT a cikin adadin kudaden.” Inji Minista Adamu.
An amince za a kallama aikin cikin shekaru biyu, tare da karin wa’adin shekara daya saboda dadewar da aka yi ba a ci gaba da aikin ba.