Shugaban Hukumar ICPC, Bolaji Owasonoye, ya bada shawarar cewa Najeriya ta rika matsa lamba kasashen da barayin gwamnatin kasar nan ke boye kudin sata, su rika biyan kasar nan kudaden ruwa idan za su maido kudaden, saboda sun amfana da kudaden.
Owasoniye ya ce idan aka bullo wa kasashen ta nan, hakan zai magance yawan satar kudade ana kimshe wa a kasashen waje (IFFs).
Shugaban na ICPC ya kara da cewa Gwamnatin Najeriya na ci gaba da duba yiwuwar sake nazari da fasalin hada-hadar fetur da gas, harajin saka jari da kuma daga kafa daga karbar harajin wasu kayan da ake shigowa da su daga waje, domin dakile lodar kudaden Najeriya ana kimshewa a kasashen waje (IFFs).
Owasanoye ya yi wannan karin haske a taron IFFs, wanda Hukumar ICPC ta shidya a Hedikwatar ICPC, a Abuja.
Ya ce yadda ake kwashe kudaden Afrika zuwa kasashen waje, ya sa nahiyar ta ci fi sauran nahiyoyi yawan fitar da kudaden su waje ta haramtacciyar hanya.
Daga nan sai ya roki kasashen da ke bin kasashen Afrika basussuka cewa su rage kudaden bashin ta hanyar rike kudaden da wasu ‘yan Afrika su ka kimshe a kasashen su. “Amma idan za su maido sauran kudaden, sai su hado da kudaden ruwa, domin sun amfana da kudaden.”
A nasa jawabin, mamba na Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya kan IFFs, Irene Ovonji-Odida, ta ce akalla manyan tantagaryar ‘yan iskan duniya sun karatar da dala tiriliyan 1.6, wadanda dala biliyan 500 zuwa 600 an yi asarar su ne wajen gaza karbar haraji, sai dala biliyan 20 zuwa 40 kuma ga bayar da cin hanci da rashawa. Sannan kuma an boye dala tiriliyan 7 a asirce cikin manyan bankunan kasashen da su ka ci gaba.
Discussion about this post