Shugaban Jami’ar Maryam Abacha, Farfesa Adamu Gwarzo ya yi jami’ar Bayero kyautar Kujerun zama na zamani.
A ci gaba da agaza wa jami’o’in Najeriya ta gidauniyar Adamu Abubakar Gwarzo yake yi, gidauniyar ta baiwa jami’ar Bayero da ke Kano kyautar manya-manyan kujeru na zama na zamani.
Wannan ba shine bane karon farko da wannan gidauniya ta Adamu Abubakar Gwarzo AAG ke yi wa jami’ar kyauta ba domin ko a watannin baya gidauniyar AAG ta baiwa jami’ar manyan motocin daukan dalibai kyauta.
Wadannan kujeru za a yi amfani da sune a sabuwar ginin Senate na Jami’ar wanda aka kaddamar ba da dadewa ba.
A cikin watan Faburairu, gidauniyar karkashin shugabancin Farfesa Adamu Gwarzo, ya mika wa jami’ar Bayero, BUK dake Kano kyautar irin wadanan motoci har guda biyar.
Haka kuma ya baiwa jami’ar Umaru Musa irin wannan bas din.
Farfesa Adamu Gwarzo ne shugaban jami’ar Maryam Abacha da ke Nijar da kuma wanda aka kafa a Najeriya, a jihar Kano.
A jihar Kaduna ma, Farfesa Adamu Gwarzo ya kafa sabuwar jami’a mai zaman kanta wanda take gab da aka kaddamar da ita.
Shugaban jami’ar Bayero ya mika godiyar sa ga shugaban jami’ar MAAUN, kuma shugaban gidauniyar AAG, bisa wannan kyauta da yayi wa jami’ar da wadanda ya yi a baya.
Ya bayyana cewa lallai jami’ar Bayero da Na Maryam Abacha za su ci gaba da yin aiki kafada da kafada a fannin yin nazari da bincike domin cigaban jami’o’in biyu.