Ina taya Juliana Bitrus murnar zama kwamishinar Lafiyar jihar Barno – Farfesa Gwarzo

0

Shugaban jami’ar Maryam Abacha, MAAUN da Jami’ar Franco-British dake Kaduna, Farfesa Adamu Gwarzo ya mika sakon taya murna ga sabuwar kwamishina kiwon Lafiya na jihar Barno, Juliana Bitrus wanda gwamna Babagana Zulum yayi.

Farfesa Gwarzo ya bayyana cewa Juliana wacce tsohuwar dalibar jami’ar Maryam Abacha ne, yayi matukar farin ciki da wannan matsayi da aka bata.

Farfesa Gwarzo ya ce da ma ita ce Kwamishinar Kula da harkokin kiwon Dabbobi da Kifi, wannan sabon nadi da aka yi mata ya dace da ita a matsayin ta na kwararriyar masaniya a fannin kiwon lafiya.

” I na ta ya kwararriyar malamar asibiti kuma masaniya a fannin kiwon lafiya da Ungozoma, sannan kuma tsohuwar dalibar jami’ar MAAUN, murnar samun wannan matsayi a jihar Barno. Ina mata fatan Alkhairi da fatan Allah ya taya ta riko ta kuma zama jakadiyar jami’ar MAAUN da za arika alfahari da aikin ta.”

Jami’ar MAAUN dake Nijar, wanda kuma ta fara aiki a Najeriya jami’ace da ta yi fice da suna a wajen karanta da dalibai ilimin kiwon lafiya, Ungozoma da aikin asibiti a nahiyar Afrika.

Daliban jami’ar sun yi fice a duk inda suke musamman a fannin kiwon kafiya, da fannonin da suka hada da nazari mai zurfi, kimiyya da fasaha da zamantakewa na zamani.

Share.

game da Author