RASHIN TSARO: Kungiyoyi 120 sun nemi a fito a yi zanga-zanga, kuma a kaurace wa shagulgulan Ranar Dimokradiyya

0

Gamayyar wasu kungiyoyi guda 120 ciki har da na masu rajin kare hakki da ‘yancin jama’a da ‘yan rajin kare dimokradiyya, sun yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya su fito kwai da kwarkwata su shiga zanga-zangar nuna rashin jin dadin kashe-kashen da ke faruwa a fadin kasar nan, a ranar 29 Ga Mayu.

Cikin wata sanarwa da gamayyar kungiyoyin su ka fitar a ranar Lahadi, sun yi kira ga ‘yan Najeriya su fito su yi jerin-gwanon nuna jimami da ta’aziyyar wadanda aka kashe da alhinin wadanda ake sacewa ana garkuwa da su a ranar 28 Ga Mayu.

Bugu da kari, sun kuma yi kira ga daukacin duk wani dan Najeriya mai kishin kan sa ya kaurace wa tarukan da gwamnati za ta gudanar domin tunawa da Ranar Dimokradiyya.

Yayin da cikin 2018 aka maida Ranar Dimokradiyya ta zama ranar 12 Ga Yuni, a wannan karo an tafka kuskuren cewa ranar 29 Ga Mayu za a yi Ranar Dimokradiyya, wato ranar ta da can da aka sani.

Sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari “ya tashi ya magance kisa, zubar da jinainai da garkuwa da mutanen da ake yawan yi bagatatan a cikin kasar nan.”

Kungiyoyin sun nuna matukar damuwar su dangane da yadda ake karya doka a oda a kowane bangaren kasar nan.

Sun kuma yi jadawalin kashe-kashe da jerin garuruwa da makarantun da aka yi garkuwa da mutane da lalata dukiyoyin da ake ci gaba da yi tun a farkon wannan shekara da mu ke ciki.

Kungiyoyin sun kira Buhari mutumin da ba ya shimfida adalci, ganin yadda ya ke tura jami’an tsaro na yin hawan-kawara kan masu zanga-zangar lumana, amma kuma ya kasa yin katabus kan ‘yan ya’adda masu yi wa jama’a kisan-gilla, masu garkuwa da kashe mutane, kananan yara da fyade ga mata.

“Abin taaici har afuwa ake bai wa irin wadannan batagari idan sun fada hannun gwamnati.”

Sun kara da cewa Gwamnatin Buhari na aikatacin amanar kasa, idan aka yi la’akari da yadda su ke jan ‘yan ta’adda a jiki, ba tare da son jama’a wannan kusanci na faruwa tsakanin gwamnati da ‘yan ta’adda.

Kadan daga cikin kungiyoyin sun hada da Action Aid. Adinya Arise Foundation, African Centre for Media and Information Literacy (AFRICMIL), Bauchi Human Right Network, CISLAC da kuma CDNDC.

Share.

game da Author