SHARAR DAJI: Sojoji sun yi nasarar kwamandojin ‘yan bindiga hudu da mayaka 48 a dazukan Zamfara da kewaye

0

A wani gagarimin farmakin kakkabe ‘yan bindiga da sojojin Najeriya su ka dauki tsawon lokaci su na aiwatarwa, sun kashe manyan kwamandojin ‘yan bindiga hudu da wasu mahara 48.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Sojojin Najeriya, Burgediya Janar Mohammed Yerima ya fitar a ranar Juma’a a Abuja, ya ce an karkashe ‘yan bindigar ne a dazukan Jihar Zamfara da dazukan jihohin da ke makautaka da Zamfara.

Ya ce an gudanar da farmakin ne domin a kakkabe ‘yan bindiga a dazukan yadda mazauna yankunan za su ci gaba da harkokin rayuwar su da noma da kasuwanci.

Yerima ya ce an karkashe kuma an tarwatsa sansanonin mahara a dazukan Jaya, Kadaya, Gabiya, Bozaye da Mereri na kusa da dazukan Maru.

“An kashe ‘yan bindiga 48 kuma sani kwamandan su mai suna Jammo ya sha harbi a kafa.

“An kuma tarwatsa sansanonin Jaya, Kaday, Bakin Ruwa da wasu sansanoni da dama.

” An ceto mutum 18 daga hannun daga hannun ‘yan bindiga, bindiga samfurin AK 47 guda takwas, samfurin G3 guda daya, PK guda daya da Mashinga ita ma daya.

“Sai kuma rangadin farmaki na biyu da aka yi tsakanin ranar 18 Ga Afrilu zuwa 3 Ga Mayu, inda aka kashe kwamandojin ‘yan bindiga da su ka hada da Yellow Mai Bille, Sani Meli, Sama’ila Ba Ka Jin Bari da kuma Dan Katsina.

“Sai kuma babban kwamandan na su mai suna Nasanda wanda ya tsere da kyar, bayan ya sha harbi.

“Sojoji sun you nasarar kwato harsasai na bindiga game-gari guda 4,600, jigidar harsasai biyu ta AK 47, harsashen AK 47 har 4,600, babur, waya kirar TECNO da sauran kaya masu hatsari.

Share.

game da Author