Shugabar Hukumar Kula da Tashoshin Ruwa, Hadiza Bala, ta karyata wani rahoto da jaridar SAHARA REPORTERS ta buga cewa ta yi amfani da mukamin ta, ta bai wa kamfanin Aliko Dangote kwangila.
Ta karyata labarin ne cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi cewa abin da jaridar ta buga ba gaskiya ba ce.
Jaridar ta zargi Hadiza da kwace ayyukan da kamfanin Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ke yi a tashoshin ruwa, ta bai wa wani kamfani mai suna ICTS, wanda a karkashin kasa Aliko Dangote aka bai wa aikin.
Shi ma kamfanin na ICTS Nigeria Ltd ya nesanta kan sa daga wata alaka da Dangote.
A raddin da ta maida, Hadiza ta ce babu yadda za a yi ta bayar da kwangila ba tare da amincewar Hukumar Gudanarwar NPA ba.
“Tun da farko ya kamata a sani cewa NPA na da tsari wanda Hukumar Gudanarwar sa ce ke yanke hukuncin duk wani lamarin da ya shafi kadarori da kasuwancin NPA.
“Saboda haka rashin mutunci ne da sharri da kuma kazafi har wani ya fito ya ce ni kadai wai na dauki wata kwangila na bayar, ba tare da amincewar Hukumar Gudanarwa ta NPA ba.” Inji ta.
Sannan kuma ta bai ma kamata a sako batun INTELS a ciki ba, saboda yarjejeniyar kwangilar sa ta fara tun cikin 2007, kuma aka kara masa wa’adin aikin tsawon shekaru 10 zai yi. To kuma yanzu tun cikin Agusta 2020 wa’adin aikin Intels ya kammala a tashar jirage ta Onne.
“An bai wa INTELS wurin tsayuwar jirage na 9, 10 da na 11 a tashar Onne cikin 2013 ba tare da wata kwakwarar yarjejeniya ba.
Hadiza ta ce cikin 2018 ta gano INTELS ba ta bai wa hukuma ko kwandala tsawon shekaru biyar, kuma INTELS ba ya amfana da tashoshin kamar yadda ya da ce.
Ta ce NPA ta nemi INTELS ta biya dukkan kudaden da ba ta biya gwamnati na karbar aron wuraren da ta yi tsawon shekaru biyar da bai biya ba. Sannan kuma ya rika amfani da wuraren kamar yadda ya dace.
“ICTNL ya sa hannun karbar kwangila har ya fara kafa kayayyaki, sai INTELS ya garzaya kotu. Kuma har yanzu shari’ar ta na kotu.” Inji Hadiza.
Discussion about this post