Gwamnatin Gombe ta gano ma’aikatan boge 431 da ke aiki a ma’aikatun jihar

0

Gwamnatin jihar Gombe ta bankado ma’aikatan boge 431 dake aiki a ma’aikatun jihar.

Da yake ganawa da manema labarai a jihar kwamishinan kudin jihar Muhammad Magaji ya bayyana cewa bayan sunayen da aka samu na karya sama da 400, an an kama wasu ma’aikata 691 da za a bincike su saboda ba su zuwa aiki kwat-kwata.

Magaji ya ce bisa ga umurnin da gwamnati ta bada na hana ma’aikata daga rukuni 1 zuwa 12 zuwa aiki saboda Kkorona gwamnati ta gano cewa ma’aikata 244 da ake biya albashin da ya kai naira miliyan 7 kowani wata ne ke karkashin wannan rukuni.

Bayan haka gwamnati ta kuma kori ma’aikata 45 dake aiki da karamar hukumar Kwami.

A dalilin haka gwamnati ta samu rarrar kudi har naira 700,000.

A karamar hukumar Kwami gwamnati za ta yi wa wasu ma’aikata hudu horo bisa kan laifin an dauke su aiki ba bisa ga ka’ida ba.

” Shugaban kungiyar kwadago NLC na jihar Bappayo Abdulmumini ya yaba wa aikin cire baragurbin ma’aikata da gwamnati ke yi a jihar.
Abdulmumini ya ce tun da gwamnati ta fara dakatar da ma’aikata babu ma’aikacin da ya kawo kara cewa an kore sha daga aiki ba bisa ka’ida ba.

Ya ce hakan na nuna cewa gwamnatita na yin aiki ne cikin gaskiya da bin doka da ka’ida.

Share.

game da Author