Mazauna karamar hukumar Zurmi sun yi banka wa fadar maimartaba Sarkin Zurmi Atiku Abubakar, wuta sanna suka jibge masa gawarwakin wadanda mahara suka kashe a kauyukan su.
Masu zanga-zangar na kokar yadda gwamnati da masarautar Zurmi ta kyale su ‘yan bindiga na kashe su kamar kaji. Sannan kuma da hana su komawa gona da ‘yan bindigan suka yi.
Wasu daga cikin wadanda suka tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA sun bayyana fushin kakara kan yadda gwamnati, jami’an tsaro da sarakuna jihar suka banzatar da su ba su basu isasshen kariya daga ‘yan bindiga da suka adda be su.
” Maharan sun rantse bana ba za mu yi noma a karamar hukumar Zurmi ba. Sun ce duk wanda ya fita noma a bakin ransa. Dole mu fito mu nuwa wa gwamnti fushin mu su san yadda za su yi da mu.
Kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu ya bayyana cewa ‘jami’an tsaro za su ci gaba da samar da tsaro a jihar, sai dai tabbas rashin tsaro ya kara yin tsanani a jihar yanzu.
” Tuni har an aika da zaratan jami’an tsaro sun nausa cikin daji domin yin farautar wadannan ‘yan bindiga, kuma za su ci gaba da zama a wannan yanki har sai zaman lafiya ya tabbata.” Inji kakakin ‘yna sanda.