Dalilin da ya sa Bill Gates da Melinda suka tsinke igiyar auren su

0

Hamshakin atajiri Bill Gates da matar sa Melinda, sun fitar da sanarwar tsinke igiyar auren su.

Cikin wata sanarwar da su biyun su ka rattaba wa hannu, kuma su ka watsa a shafin su na twitter, Bill da Melinda sun ce daga ranar Litinin babu sauran igiyar aure a tsakanin su.

“Bayan mun yi nazari da zurfin tunani, mun amince a tsakanin mu cewa ba za mu iya ci gaba da kasancewa miji da mata ba.

“Mun shafe shekaru 27 a matsayin miji da mata, har mu ka haifi ‘ya’ya uku. Kuma mun kafa Gidauniyar Bill & Milinda wadda ta shahara wajen samar wa miliyoyin al’umma ingantacciyar lafiya a duniya.”

Bill ya auri Melinda cikin 1994 bayan sun hadu a taron Hada-hadar Cinikayya ta Duniya a birnin New York na Amurka.

Melinda ta fara aiki a kamfanin Bill na Microsoft, amma ta ajiye aiki bayan shekara biyu, a 1996, saboda bukatar zaman gidan miji.

Cikin shekarar 2000 sun kafa Gidauniyar Bill&Melinda Gates, wadda daga farkon kafa ta zuwa 2021, ta kashe kudade wajen ayyukan jinkai da agaji a fadin duniya har na dalar Amurka bilyan 50.

Bill Gates ya taba zama hamshakin attajirin da ya fi kowa kudi a duniya, har na shekaru masu dama, kafin yanzu ya koma na hudu a jerin attajiran duniya.

Share.

game da Author