RADDIN MBAKA GA BUHARI: Ba ka dai ba ni kwangila ba, na fi karfin ka goranta min

0

Babban Limamin Kirista aminin Shugaba Muhamadu Buhari, wanda su ka raba hanya kwanan nan, ya fitar da zazzafan raddi ga Fadar Shugaban Kasa, bayan ta fallasa cewa kwangila ya nema bai samu ba, shi ya sa ya huce-hauci kan Buhari har ya ke cewa ko dai ya sauka, ko kuma Majalisar Dattawa ta Tsige shi.

A raddin da Ejike Mbaka ya maida wa Fadar Shugaban Kasa, ya ce, “Ina mai godiya matuka tunda dai ba ku ba ni kwangila ba ballantana ku goranta min.” Inji Mbaka, wanda ya furta haka cikin wani bidiyon sa da aka fitar a ranar Litinin, a gaban dandazon magoya bayan sa, yayin ibada a farfajiyar cocin sa.

Mbaka bai yi musun neman kwangila ba, amma ya ce kwangilar ba ta sa ba ce, wasu mutane ne su uku su ka nemi ya hada su da Fadar Shugaban Kasa domin a ba su kwangilar aikin kayan samar da tsaro na zamani.

“Ban san mutanen nan ba, sun zo Enugu sun nemi na hada su, kuma na kai su, ba ni a cikin kwangilar, kuma ban san yadda su ka karke ba.

“Abin ya faru tun zangon Buhari na farko, na kai su a lokacin na hada su da Abba Kyari. A tsayuwar nan da na ke a gaban su, na rantse da Ubangiji ko lambar wayar su ba ni da ita.

“Kuma mene ne aibi? Mutanen sun nuna su na da fasahar tsarin ayyukan kayan tsaro na zamani. Sun nemi a ba su aiki domin su samar da dabarun tsaro. Ni ma na ga idan na hada su, to na taimaka an samu tsaro kenan.

“To ni wa ya isa ya yi min gorin wata kwangila? Fadar Shugaban Kasa ta kuwa san ni kowa ne kuwa? Shin sun san yawan mabukatan da na ke ciyarwa? Sun san yawan zawarawan da mazan su sun mutu ni ke biya masu kudin haya su da ‘ya’yan su? Shin sun san yawan daliban da na ke biya wa kudin makaranta a ciki da wajen kasar nan?

“Ni fa ni kadai ne tallin-tal di na, ba ni da mata, ba ni da ‘ya’ya ko daya. Ashe idan har zan rika yin irin wannan kokarin, sai dai ni na yi wa Gwamnatin Buhari gorin ta kara kokari wajen kula da marasa galihu.

“Amma sun fi maida hankali wajen kimshe kudaden da za su yi kamfen din zabe da su. Ai na sa san komai. Na yi bakam ne ina kallon su. Jira na ke kawai Ubangiji ya sanar da ni lokacin fallasawa, sannan ni kuma zan fito na fallasa su.” Inji Mbaka.

Share.

game da Author