BINCIKEN KUDADEN SATA: Majalisar Tarayya ta umarci Akanta Janar ya bayyana cikin sa’o’i 48, domin a sakato fam miliyan 5 cikin kogon hakori

0

Majalisar Tarayya ta bai wa Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris wa’adin ya bayyana a gaban ta cikin sa’o’i 48, domin yin bayanin salwantar wasu kudaden satar da aka kwato a hannun wasu barayin gwamnati, da yanzu kuma ake so a sakato su a cikin kogon hakoran wasu sabbin barayin gwamnatin.

A ranar Talata dai Idris ya bayyana a gaban Kwamitin Binciken Halin da Kudaden Satar da aka Kwato ke Ciki.

Idris dai ya kasa yin gamsasshen bayanin yadda aka samu baddalallun alkaluman kudade tsakanin wadanda ya gabatar wa Kwamitin Bincike da kuma kwafen takardar adadin kudaden da Babban Bankin Najeria, CBN ya bai wa Kwamitin Majalisa.

Misali, Idris ya kasa yin bayanin inda wasu zunzurutun fam miliyan 5 su ka makale. Wani Dan Majalisa, Edun Oladapo dan APC daga Jihar Ogun ne ya tayar da ballin.

Ganin yadda ya kasa yin bayani a gaban kwamiti kan kudaden ne, sai Honorabul Oladipo ya nemi a gayyaci Idris ya bayyana a gaban ‘yan majalisar baki dayan su domin ya yi masu gamsasshen bayani.

Sai dai Honorabul Wole Oke ya nemi a bai wa Akanta Janar Idris lokacin da zai koma ya yi bincike domin ya gano inda kullin ya kwance.

“Jama’a shi rakod fa ba ya karya. Babu yadda za a yi fam miliyan 5 su bace kamar garin toka ya bi iska. Mu ba shi lokaci mana ya je ya bincika.” Inji Oke.

Idris ya yarda a ba shi lokaci, inda aka amince ya koma ya bayyana a ranar Alhamis.

Share.

game da Author