Najeriya, Faransa da wasu kasashe sun la’anci juyin mulkin Mali

0

Shugabannin duniya sun yi Allah-wadai da sojojin da su ka yi juyin mulki a Mali, wadanda su ka kifar da Gwamnatin Rikon Kwarya ta Shugaba Bah Ndaw da Firayi Minista Moctar Ouane.

Sojojin juyin mulki sun zargi Shugaba da Firayi Minista da laifin yi wa gwamnatin rikon ƙwarya zagon ƙasa.

Sojojin sun ce za su ci gaba da shirya zaben mika mulki a hannun farar hula cikin 2022, kamar yadda aka tsara tun farko.

An kama shugabannin biyu tare da Ministan Tsaro, Souleymane Doucoure, a juyin mulkin kasar wadda zaman lafiya ya yi wa karanci matuka.

Wannan ne juyin mulki na biyu a Mali, a cikin watanni tara.

An naɗa Ndaw da Ouane domin su shirya zabe cikin watanni 18 domin gaggauta komawa a mulkin farar hula a Mali.

Cikin watan Maris, 2021 aka shirya za a gudanar da zaben.

Amma shugaban juyjn mulkin, Kanar Assimi Goita, ya zargi shugabannin biyu da laifin rashin iya shugabanci ta hanyar kasa magance zanga-zangar da aka shafe sama da mako daya a jere ana yi a Mali.

Goita na cikin wadanda su ka shirya juyin mulkin farko. Ya ja baya ne bayan kasashen duniya sun matsa masa lambar amincewa a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya, wadda ya nada kan sa Mataimakin Shugaban Kasa.

Shi ne kuma yanzu ya sake kwace mulkin kasar.

Share.

game da Author