Mahara sun kashe’ Yan banga 21 da Dagaci 1 a Sokoto

0

Mahara sun kashe ‘Yan banga 21 da wani wani Dagaci a hari da suka kai wa Kauyen Yartsakuwa da ke karamar hukumar Rabah, jihar Sokoto.

‘ Yan bindigan sun kashe Dagacin Sabon Birni ranar Talata bayan sun tare hanyar Sabon Birni zuwa Shinkafi, inda suka yi wa matafiya da dama fashin kaya da miliyoyin kudi da shanu masu yawa.

Gwaman jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya ziyarci garin inda ya jajanta wa yan uwa da iyalan yan bangan da maharan suka kashe.

Tambuwal ya kara da cewa ” Gwamnati zata sake fasalin aikin yan sakai a jihar ta hanyar inganta shi. Za mu siya musu babura da naurar sadarwa domin kai rahoton duk abinda ke faruwa.

Bayan nan Tambuwal ya ce za a rika biyan su dan wani abu domin su rika jika makoshi kan abinda suke yi na kare al’umma.

Sannan kuma ya ce gwamnatin jihar za ta dan tallafawa iyayen matasan da suka rasa rayukan su a wannan arangama da yan bindiga domin su rage zafin rashin da suka yi.

Share.

game da Author