ZAZZABIN CIZON SAURO: Gwamnati ta raba gidajen sauro 1,000 kyauta a jihar Anambra

0

A shekarar 2020 gwamnatin jihar Anambra ta raba gidajen sauro 1,000 wa yara ‘yan makaranta da mata masu ciki a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar Vincent Okpala ya sanar da haka ranar Talata a garin Awka.

Okpala ya ce sakamakon bincike da dama da WHO ta gudanar sun nuna cewa har yanzu zazzabin cizon sauro na kashe yaro daya a cikin minti biyu a duniya.

Ya ce a dalilin haka WHO ta yi kira ga gwamnatocin kasashen duniya su inganta fannin kiwon lafiyar su domin kare lafiyar yara kanana.

” Kwana a cikin gidan sauro na cikin hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar saboda haka gwamnati ta raba gidajen sauro 86,000 wa yara ‘yan makaranta da 15,000 ga mata masu ciki a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da manyan asibitocin jihar.

Okpala ya yi kira ga mutane da su shiga tsarin inshoran lafiya ta jihar domin samun lafiya a farashi mai sauki.

Ya ce duk wata, mutum zai rika biyan naira 1000 wa inshorar ko kuma naira 12,000 a shekara.

“Idan an kamu da zazzabi a rika zuwa asibiti ne likita ya duba mutum, a kuma karbi magani amma ba a zauna a gida ana shan magani batare da izinin likita ba.

Bayan haka shugaban Shirin dakile yaduwar zazzabin cizon sauro na jihar Nonso Ndudi ya ce wannan shiri ya taimaka wa gwamnati wajen rage yaduwar cutar a jihar.

Ndudi ya ce wayar da kan mutane game da mahimmancin tsaftace muhallin da amfani da gidajen sauro ya taimaka wajen nasarar da aka samu.

Share.

game da Author